Jarin da Sin ta zuba a fannin binciken kimiyya zai iya kaiwa kusan Yuan tiriliyan 2.79 a shekarar 2021

Daga CRI HAUSA

Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar ƙasar Sin ya gudanar da taron ’yan jaridu a yau, inda ya gabatar da ci gaban da aka samu a fannonin kimiyya da fasahar ƙirƙire-ƙirƙire na ƙasar.

Game da jimillar ci gaban da fannin ayyukan kimiyya da fasaha na ƙasar Sin ya samu a shekarar 2021, an gabatar a wajen taron cewa, jimillar jarin da aka zuba a fannin bincike da bunƙasa ci gaban kimiyya da fasaha, ya kai RMB Yuan triliyan 2.79, wato an samu ƙarin kashi 14.2 bisa 100, sama da na shekarar 2020, kuma jimillar alƙaluman jarin da aka zuba a fannin bincike da raya cigaba, wato R&D, idan an kwatanta da matsayin GDPn ƙasar, ya kai kashi 2.44 bisa 100, sannan gundarin kuɗaɗen da aka zuba ya ƙaru da kashi 15.6 bisa 100 idan an kwatanta da na shekarar 2020, yayin da jimillar adadin jarin na R&D ya kai kashi 6.09 bisa100, kuma cikakken girman matsayin ƙirƙire-ƙirƙire na ƙasar Sin ya ƙaru zuwa matsayi na 12 a duniya.

Fassarawa: Ahmad Fagam