Jarumi Kanayo O. Kanayo ya gargaɗi masu fim kan yadda suke yaudara ta hotuna da kwalliya a finafinansu

Daga AISHA ASAS

Shahararren ɗan wasan fim a masana’antar Kudu, wato Nollywood ya gargaɗi masu shirya finafinai kan yadda suke bayyana ababen da ke voye gaskiyar rayuwa ta mutanenmu, ta hanyar amfani da aiki daban da abinda yake zahiri, tare kuma da kwaikwayon ababen da suka bambanta da ababen da muka sani, wanda hakan ke kai masu kallo ga ruɗani kan wanene daidai, tsakanin gaskiya da kuma abinda ake nunawa, yayin da ta wani vangaren zai iya zama silar rashin tagomashin finafinan, dalilin gyara da mai kallo zai ta cin mai shiryawa.

Jarumin ya yi wannan kira ne a ranar Talatar da ta gabata a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya ce, da yawa daga cikin masu shirya finafinai ba sa amfani da kayan da al’adunmu suka tanada a cikin shirin fim ɗin su, kuma ba sa bayyana gaskiyar rayuwa a hotunan jaruman da suke haskawa.

“Da yawa daga cikin masu shirya fim na yi wa hotunan finafinansu fentin da bai dace da su ba, duk a ƙoƙarin haskaka hotun, wanda hakan na bayar da bauɗaɗiyar ma’ana ga masu kallo,” inji shi.

Jarumin ya qara da cewa, “da yawa daga cikin masu aikin fim sun jahilci dalilin yin sa, domin ɗaya daga cikin ajendar ƙirƙirar finafinai akwai yaɗa al’addu da ɗabi’un jama’a, ta yadda ake iya gane kowanne ɓangare da shiga da kwalliyar da mutanen ke yi a finafinan.”

Kanayo ya ci gaba da bayyani kan yadda ake nuna shiga da bata dace da lokacin da ake son nunawa ba, kamar sanya kayan da ake fita da su na alfarma a zauna a gida, ko haska macen da take a mawucin hali ko aiki irin na girki da kwalliya, alhali a zahiri hakan ba za ta kansace ba a zahiri.

“A wani lokacin za ka ga an nuna mai kuɗi yana zaune a gidansa, amma ya yi shiga irin ta fita, agogo, takalma, Tshirt, saɓanin a gan shi da Agbada. Ta yaya zai yiwu ace namiji na zaune gida yana hutawa, amma ka gan shi kamar yana shirin zuwa biki, ko kuma mace ta sha ado, sannan ta shiga madafi don yin girki. Ko kuma mace ta kwanta barci, amma fuskarta ɗauke da kyakykyawar kwalliya,” inji jarumin.

Daga ƙarshe Kanayo O. Kanayo ya bayyana muhimmancin haska hoto daidai da abinda ake ƙoƙarin bayyanawa, wanda ya ce, hanya ce ta ɗaga darajar finafinai da samar da cigaba mai yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *