Jayati Ghosh: Manufofin kuɗi na Amurka suna haddasa haɗari ga sauran ƙasashe

Daga CMG HAUSA

Jayati Ghosh, farfesa a fannin tattalin arziki a jami’ar UMASS Amherst ta ƙasar Amurka, ta bayyana wa ‘yan jarida a kwanakin baya cewa, manufofin kudi na tsuke bakin aljihu da baitulmalin ƙasar Amurka ya fitar, suna haddasa haɗari ga sauran ƙasashe, kana ba za su iya tabbatar da warware matsalar hauhawar farashin kaya da ƙasar Amurka take fuskanta ba.

Ghosh ta bayyana cewa, tsauraran manufofin kuɗin na baitulmalin Amurka, za su haddasa janye jari daga ƙasashe masu tasowa da kwarara zuwa ƙasar Amurka, hakan zai haddasa rikicin basussuka da haɗarin rikicin musayar kuɗi a yankuna da dama na duniya.

Ta kara da cewa, a halin yanzu, ƙasashe masu tasowa da dama ba su farfaɗo daga cutar COVID-19 ba, kana suna fuskantar matsin lamban raguwar saurin bunƙasuwar tattalin arziki, kuma matakan ƙara kuɗin ruwa da baitulmalin ƙasar Amurka ya ɗauka, za su tsananta matsalolin hauhawar farashin kaya a waɗannan ƙasashe.

A halin yanzu, farashin abinci da mai ya tashi a ƙasashe masu tasowa da dama.

Ghosh ta yi imanin cewa, a cikin goman shekaru da suka gabata, ƙasar Amurka ta kasance tana yin amfani da ikon musamman na kuɗin dala a matsayin kuɗin ajiye na duniya don buga kuɗin ba bisa ƙa’ida ba, ko kuma sanya takunkumi kan wasu ƙasashe ba bisa dokokin duniya ba, waɗannan ayyuka sun zubar da kimar ƙasar Amurka a idon duniya.

Fassarawar Zainab

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *