Jerin ƙasashe da ke bai wa maza tallafi don auren matan ƙasarsu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ga maza masu sha’awar yin aure, wasu ƙasashe suna bada tallafi mai ƙarfi da sauran abubuwan ƙarfafawa a ƙoƙarin ƙara yawan jama’a da samar da daidaiton jinsi.

Chisom Michael ya rubuta cewa ana ba da tallafin kuɗi ga ɗaiɗaikun mutane, musamman maza daga waje, waɗanda ke auren matan ƙasashen da nufin magance ƙalubalen ƙarancin jama’a da kuma farfaɗo da al’umma.

Ko da yake akwai bambance-bambance a cikin manufofi, amma babbar manufar ita ce magance ƙarancin jama’a da samar da daidaiton jinsi don ba da gudunmawa ga ƙaruwar yawan jama’a wanda hakan zai ƙara haɓaka tattalin arzikin ƙasashen.

A cikin jerin da Eightify suka tattara, ga ƙasashe bakwai da ke ba da tallafin kuɗi don aurar da matansu;

1. Chana;

ƙasar Sin na fama da ƙarancin haihuwa, sakamakon dokarta na haihuwar ɗa ɗaya da ta saka a shakarun baya, wadda ba da jimawa ba aka sassauta dokar. Don kawar da ƙarancin jama’a, gwamnatin ƙasar Sin ta ɓullo da wasu shawarwari daban-daban. ɗaga daga ciki shi ne bayar da Yan 1,000 (kimanin dala 1,370) a matsayin tallafin kuɗi ga mazan da suka auri mata masu shekaru 25 ko sama da haka.

Wannan manufar tana da nufin ƙarfafa auren farko da kuma ƙara yawan al’umma. Waɗannan yunƙurin wani ɓangare ne na dabarun da aka tsara don haɓaka al’ummar ƙasar da rage yawan tsufa.

2. Hungary;

ƙasar Hungary ta aiwatar da matakai daban-daban don ƙarfafa aure da haɓaka yawan jama’arta. Gwamnati tana bada tallafi tare yafe bashi ga ma’auratan da ke da ‘ya’ya biyu ko fiye da haka. Wata sanannen manufa ta haɗa da bayar da lamuni mara riba na Yuro 30,590 ga sababbin ma’aurata.

An yafe wannan lamunin gabaɗaya bayan haihuwar ɗansu na uku. Waɗannan abubuwan ƙarfafawa suna da nufin haɓaka haihuwa a Hungary ba tare da dogaro da wani abu ba.

3. Italiya:

Italiya, musamman a yankunan karkara, na fuskantar raguwar yawan jama’a da rashin daidaiton jinsi. A yankuna kamar Candela da Dormina, 1ananan hukumomi suna bada gudu!mawar kuɗi don jawo hankalin sababbin baƙin ƙasar wajen ƙarfafa musu auren ‘yan matan yankin.

4. Iceland;

Iceland ƙasa ce da ba ta da yawan jama’a tare da ƙalubalen ƙaramin yawan maza. Domin magance wannan rashin daidaito, an yi ta raɗe-raɗin cewa ƙasar na bayar da tallafin kuɗi ga mazaje na ƙasashen waje da suka auri matan Iceland, inda rahotanni ke nuna cewa ana biyan dala 5,000 duk wata.

Kodayake sau da yawa ana muhawara game da halaccin wannan abin ƙarfafawa, Iceland ta fahimci buƙatar haɓaka yawan jama’a kuma tana ƙoƙarin ƙara yawan al’ummarta wajen haɗin gwiwar aure da maza daga ƙasashen waje.

5. Estoniya;

Estonia, ƙaramar ƙasa a gabashin Turai, tana bada taafi iri-iri don jawo hankalin baƙi, musamman waɗanda ke son auren matan ƙasar. Gwamnatin Estonia tana bada tallafin kuɗi, tare da samar da kiwon lafiya da ilimi kyauta ga ma’auratan da ke zaune a ƙasar.

Wannan yunƙuri wani ɓangare ne na dabarun Estonia don inganta yawan jama’a.

6. Rasha;

Rasha na fuskantar manyan ƙalubalen yawan jama’a, da suka haɗa da raguwar yawan haihuwa da rashin daidaiton jinsi, inda mata suka fi maza yawa. Dangane da mayar da martani ga ƙalubalen, gwamnatin Rasha ta ɓullo da wasu abubuwan ƙarfafa gwiwa da nufin ƙarfafa aure da ci gaban iyali.

Waɗannan sun haɗa da tallafin gidaje da rage haraji ga ma’aurata.

7. Denmark;

Denmark ta zama sananniyar ƙasa ga ma’aurata na duniya saboda sauƙaƙa tsarin aure tsarin yayin da kuma suke maraba da auren mazan daga ƙasashen waje.