Jerin kadarorin da gwamnatin Buhari za ta cefanar don yin ciko a kasafin kuɗin baɗi

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasar Nijeriya, Muhammadu Buhari ta fidda wani jerin sunayen kadarorin gwamnati guda 25 da za ta sayar don yin cikon giɓin Naira tiriliyan 10.7 a kasafin kuɗin Nijeriya na shekarar 2013.

Daga cikin waɗannan kadarorin 25, wasu an sayar da su ne, yayin da wasu kuma aka rarraba hannun jarinsu aka sayar domin dai a samu a yi ciko a wannan kasafin kuɗin da yake neman kasawa.

Idan ba a manta ba da ma, Buhari ya tava faɗa cewa, Naira tiriliyan 10.7 ɗin da ta kasa a cikin kasafin kuɗin shekara mai zuwa, 2023 za a nemo cikinsa ne ta hanyar rance da kuma sayar da wasu kadarorin ƙasa don ɗaukar nauyin wasu manyan ayyuka.

Shugaban ya ba da wannan sanarwar ne a ranar Juma’ar 7 ga watan Oktoba na shekarar 2022, a yayin da yake gabatar da kasafin kuɗin a gaban Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai a wani taron haɗin gwiwa da aka yi a majalisar dokoki ta ƙasa. Shi dai wannan kasafi rahotanni sun bayyana cewa, ya ɗara na bara ne da Naira tiriliyan uku kawai.

A cewar wata majiya, daga ma’aikatar Kuɗin da Kasafi da tsare-tsaren ƙasa, gwamnati tana shawarar sayarwa ko rarraba hannayen jari na dandalin Tafawa Balewa Square dake Legas, Hakazalika, dukkan cibiyoyin samar da makamashi ta amfani da ruwa da suke a faɗin ƙasar nan. Kamar, waɗanda suke Oyan Usuma, Katsina-Ala da Giri plants. Akwai kuma babbar Kasuwar Bajekolin Legas a ciki.

Waɗannan kaɗan ne daga kadarorin da gwamnatin take da burin sayar da su ko mayar da su hanyoyin samar da kuɗi ga gwamnatin Tarayyar.

Wasu kuma za a sayar da su ne kawai don a rage asara. A cewar gwamnatin Tarayya, gwamnatin ba wani amfani za ta yi da waɗancan kuɗaɗen da aka cefanar da kadarorin nata ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *