Jerin matan marigayi Oba na Oyo guda 13 da ‘ya’yansa

Daga AISHA ASAS

A ranar Juma’ar da ta gabata, 22 ga Afrilu, 2022, Jihar Oyo ta yi rashin jigo kuma smbasarakenta, wato Alaafin Oba Lamidi Adeyemi. Ya rasu yana da shekaru 83. Shekara 52 da hawansa karagar mulki.

Marigayin ya kasance na farko a tarihin masarautun Nijeriya na wannan zamani da ya tara adadin matan aure 13 da suke ƙarƙashin ikonsa.

Kafin mutuwar basaraken, ya ɗaura aure da mata ɗaɗaya har 13, ciki kuwa har da ‘yar ƙabilar Ibo da ya aura a shekarar 2020 kuma amarya daga cikinsu, wato ta cikon sha uku.
Oba Lamidi Adeyemi ya zama Alaafin na farko a ƙabilar da ya taɓa auren wata mata da ba Bayara ba, wato a lokacin da ya auri matar tasa ta 13, Olori Chioma. Sauran matan sun haɗa da:

Olori Ayaba Abibat Adeyemi (Uwar gida)
Olori Rahmat Adedayo Adeyemi
Olori Mujidat Adeyemi
Olori Rukayat Adeyemi
Olori Folashade Adeyemi
Olori Badirat Ajoke Adeyemi
Olori Memunat Omowunmi Adeyemi
Olori Omobolanle Adeyemi
Olori Moji Anuoluwapo Adeyemi
Olori Damilola Adeyemi
Olori Chioma Adeyemi

Ragowar mata biyu kuwa ba bayyanin sunayensu duk da cewa an san da zamansu, kasancewar ba dukka matan nasa ne yake yawo da su ba, kuma ba duk 13 ne ke zaune a masarautar ba.

A wata tattaunawar da jaridar PUNCH ta yi da basaraken a shekarar 2018, ya bayyana yadda yake auren matayen nasa, inda yake cewa, “Babu ɗaya daga cikin matayena da na nemi auren kan kaina. Su ke nuna sha’awar zama tare da Ni bayan na na ba su ilimin zamani. A lokacin da suka kammala jami’a, na kan ce su tafi don yin rayuwarsu, amma sai su ƙi, su zaɓi zama da Ni. Kuma ƙarancin karatun da Matana suke da shine babbar diploma.

Ba na cin zarafin mata ko yi masu wani abu da bai dace ba. Aure abu ne mai matuƙar muhimmanci, kuma kowa na da irin rawar da zai iya taka wa ta inganta zamantakewar auren.

Kowacce mata daga cikin matana tana da muhimmanci, kuma ni Ubangiji ya ba ni baiwar iya riƙe mata, musamman kyawawan mata. Bana munafurci tsakanin matana, duk abin da ɗaya ta sanar da ni ba na mayar da shi gulma ga wata matar.

A matsayina na shugaba, dole in zama abin koyi ga al’umma, domin Ni ne madubin dubawarsu. Matana suna samun matsala tsakanin su, sai dai ubangida ya hore min sanin hanyoyin da zan bi don kashe wutar rigimar tun bata girmama ba.”

Game da yadda ya yi aurensa na farko kuwa, basaraken ya ƙara tsayawa kan furucinsa na farko na bai taɓa neman auren wata ba, inda yake cewa, “Ban taɓa gaba da gaba da mace da sunan soyayya ba, matata ta farko ƙawar ƙanwata ce da ta mutu, ita ce ta haɗa mu. Duk da cewa matata ta farko ba ta yi karatu ba, ta haifa mun lauya na farko a cikin zuri’ata.”

Ta ɓangaren adadin ‘ya’yan marigayin kuwa, har zuwa yanzu babu takamaiman adadin yawansu, duk da cewa wata majiya na cewa 20 ne, wasu daga cikin matan sun haifi yara ɗaya ne, yayin da wasu ke da fiye da hakan, har waɗanda ba su haihu ba akwai a cikinsu.

Wasu daga cikin ‘ya’yan nasa da suka yi shuhura akwai Babatunde Israel Adeyemi, Gimbiya Folashade Adeyemi da kuma Yarima Akeem Adeyemi. Dukkansu sun yi suna a ɓangarorin nasu. Babatunde Israel Adeyemi ya kasance cikakken lauya kuma fasto. Yayin da Gimbiya Folashade Adeyemi ta kasance babbar ‘ya mace a gidan kuma babbar ‘yar kasuwa, shugabar mata ta Jihar Oyo kuma shugabar Arewa House of Culture.