Jerin mazaɓu 240 da INEC ta ce ba za a gudanar da zaɓe a cikinsu ba

Daga WAKILINMU

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta fitar da jerin sunayen mazaɓun da ta ce zaɓe ba zai gudana a cikinsu ba saboda rashin rijistar masu kaɗa ƙuri’a.

Tun da fari, Shugaban INEC na Ƙasa, Mahmood Yakubu, ya bayyana a ranar Litinin cewa mazaɓun da lamarin ya shafa ba su da mutum ko guda da aka yi wa rijistar zaɓe a ƙarƙashinsu.

A cewarsa, baki ɗaya mazaɓu 176,606 ake da su a faɗin ƙasa.

Ya ƙara da cewa, waɗanda aka sauya wa mazaɓa za su samu saƙon tes ta waya mai ɗauke da bayanin mazaɓar da aka tura mutum kafin lokacin zaɓe.

A Janairun da ya gabata INEC ta bayyana adadin masu zaɓen da ta yi wa rijista a faɗin ƙasa wanda ya kama mutum 93,469,008, wanda su ne ake sa ran za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen na 2023.

Manhaja ta binciko jerin sunayen mazaɓu 240 da kanarin ya shafa, ga su kamar haka: