Jerin sunayen ɗalibai 17 da aka sace a jami’ar Greenfield

Daga AISHA ASAS

An saki sunayen ɗalibai su 17 da aka yi garkuwa da su a Jami’ar Greenfield mai nisan kilomaita 34 da ke babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wani ma’akacin jami’ar da ya buƙaci a sakaya sunansa, shi ne ya bayyana sunayen ɗaliban da lamarin ya shafa.

Ma’akacin ya faɗa cewa ɗaya daga cikin masu gadin makarantar ya rasa ransa yayin harin wanda ya auku ranar Talata, 20 ga Afrilun 2021.

Ga dai jerin sunayen ɗaliban da ‘yan bindigar suka sace wanda baki ɗayansu maza ne babu mace ko guda:

1 Abraham Akinje

2 Fortune Alhassan

3 Miracle John

4 Miracle Turman

5 Jesse Jakiri

6 Joseph Davies

7 Abdullahi Yusuf

8 John Yari

9 Michael Samson Ladan

10 Abdulkareem Ibrahim

11 Kabir Hamisu

12 Lemuel Adamu

13 Israel Antonio

14 Israel Musa

15 Nelson David

16 Mariam Nalado

17 Abdulkadir Abubakar

Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari Rundunar ‘Yan Sandan Kaduna ba ce komai ba kan wannan batu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *