Jihar Kaduna ta buƙaci a ƙara mata kujerun aikin Hajjin 2023

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A daidai lokacin da ake ci gaba da kokawa a kan tsadar kuɗin kujerar Aikin Hajji, Jihar Kaduna, wacce aka ba kujeru mafi yawa a bana, ta buƙaci a ƙara mata guda 500.

Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar, Dokta Yusuf Yakubu Alrigasiyyu ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kaduna, ranar Talata.

Ya ce sun aike da buƙatar ce saboda su ba ɗimbin mutanen da suke son biyan kuɗaɗensu a jihar yin hakan.

Idan za a iya tunawa, Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ware wa jihar kujeru 5,987 daga cikin adadin da Saudiyya ta ba Nijeriya a bana, kuma ana sa ran kowannensu zai biya Naira miliyan 2 da dubu 900.

Ya kuma ce duk maniyyacin da ya biya kuɗin, za a ba shi kuɗin guzuri har Dalar Amurka 800.

Shugaban ya kuma bayyana dalilai da dama a matsayin waɗanda suka haifar da ƙarin kuɗin kujerar a bana da suka haɗa da tsadar masauki a ƙasar Saudiyya da tsadar farashin canjin Dala da ta man jirgi da kuma ƙarin harajin VAT da Saudiyya ta yi zuwa kaso 15 cikin 100.

Sai dai ya ce duk da ƙarin da aka yi na bana, kuɗin kujera a Nijeriya na ɗaya daga cikin waɗanda suka fi arha a faɗin duniya.

Dokta Yusuf ya ce akwai ƙasashe irin su Malaysia da Pakistan da Ghana da kuma Jamhuriyar Nijar da ke biyan kuɗaɗe sama da na Nijeriya.

Ya kuma yaba wa shugabancin hukumar NAHCON saboda tabbatar da cewa duk da waɗancan dalilan, kuɗin kujerar bai ma kai Naira miliyan uku ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *