Jihohi 7 sun janye ƙarar da suka shigar kan nasarar Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Bakwai daga cikin jihohi takwas da suka shigar da ƙara Kotun Ƙoli suna ƙalubalantar nasarar sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, sun janye ƙarar tasu.

Sun janye ƙarar ne a ranar Juma’a, tare da miƙa wa kotun sanarwar janye ci gaba da shari’ar.

Jihohin da lamarin ya shafa, da suka haɗa da Adamawa, Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Edo, Taraba da kuma Sakkwato sun cimma wannan matsaya ne ta tawagar lauyoyinsu ƙarƙashin jagorancin Chief Mike Ozekhome (SAN).

“Kotu ta sani cewa masu ƙara sun yanke janye ƙarar da suka shigar kan wanda ke kare kansa,” in ji sanarwar.

Sai dai kuma, babu wani cikakken bayani kan dalilin da ya sa jihohin suka ɗauki matakin janye ƙarar.

Da fari jihohin da lamarin ya shafa sun shigar da ƙara Kotun Ƙoli ne inda suke ƙalubalantar yanayin tattara sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gudana a jihohi 36 har da Abuja wanda hukumar zaɓe, INEC, ta gudanar a ranar Asabar ta makon jiya.

Sun yi ra’ayin cewa tsarin da aka bi wajen tattara sakamakon ya saɓa wa Dokar Zaɓe ta 2022.