Jiki da jini…

Daga MUSTAFA IBRAHIM ABDULLAHI

Yan uwa masu karatu Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai ilmintarwa, da ke zayyano muku bayanai game da duniyar jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, kuma ku san yadda jikinku ke aiki.

Malam bahaushe na cewa jiki da jini sai da Hutu. To amma jikin ɗan Adam kusan koyaushe colin aiki yake. Duk ranar da ya tsaya cak, to tabbas rayuwa ta ƙare. Sai dai kuma hakan ba ya nufin jikin ɗan Adam ba ya buƙatar hutu. Zanfi mayar da hankali wajen bayyana ayyukan jiki.

Taken rubutunmu na yau shi ne kaifiyyar yadda jikin ɗan adam ke aiki. Haƙiƙa wannan fanni ne mai faɗi, saboda wasu sassa na jikin ɗan adam suna gudanar da ayyukansu ne ta keɓantacciyar hanyar da su kaɗai ke bi; sannan kuma wasu sassan irin su ƙwaƙwalwa, har yanzu ba a qure ayyukan da take yi a jikin ɗan adam ba. Saboda haka wannan fage ya na da faɗin gaske matuƙa. Amma dai zanyi ƙoƙari na kawo yadda jiki ke aiki a dunƙule, kafin muga yadda wasu sassan jikin ke gudanar da kevantattun ayyukan nasu.

Da farko dai ina so in fara da muhimman ɓangarori guda biyu waɗanda su ne ke kula da duk wata harƙallar aikin da ke faruwa a jikin ɗan adam. Na farko shi ne sashen da ke kula da shige da ficen saƙonni da kuma tsarawa da gudanar da jikin ɗan adam. Na biyu kuwa, shi ne sashen kula da feso da wasu sinadarai da ake kira “hormones”.

Bari mu fara da na farkon, wato sashen da ke kula daidatawa da gudanar da jikin ɗan adam. Wannan sashe yana ƙarƙashin kulawar ƙwaƙwalwa da laka, tare da jijiyon motsi da suka fita daga jikinsu. Su jijiyoyin su na da alaƙa da kusan kowanne sashe na jikin ɗan adam kuma su ne ke sarrafa duk irin motsi da aikin da wannan sashe ke gudanar.
Ɓangare na biyu shi ne mai kula da tasarrufi da feso sinadaran kemikals da ake kira “hormones” a turance. Shima babban jigo ne a ayyukan jikin ɗan Adam kuma abokine ga ɗaya sashen da na fara ambata.

Waɗannan ɓangarori guda biyu su ne a tsaye wajen kula da duk wani abu da ke faruwa a jiki, ko kuma abubuwa na waje waɗanda ke da tasiri akan jikinmu. Misali: yanayi na murna ko akasin haka, girma, balaga, tsufa, ɗabi’a, tafiya, bacci, magana, saduwa, gudu, da sauransu.

A mafi yawan lokuta, waɗannan ɓangarori biyu su na aiki tare wajen tafiyar da ayyukan jiki; sai dai sun sha banban a yadda sigar aikin kowanne yake.

Shi ɓangaren gudanar da al’amuran jikin ɗan adam yana aiki ne ta hanyar kai-kawon saƙon lantarki wanda hakan ke kawo sauyi a jikin ɗan adam. Misali: idan mutum ya taka qusa,to za a ɗauki saƙon lantarki daga ƙafarsa ko ƙafarta izuwa cibiyar gudanarwa da bada umarni ta jiki, wato ƙwaƙwalwa. Idan saqon yaje, ƙwaƙwalwa za ta fayyace shi, ta fassara shi, sannan ta turo umarnin matakin da za a ɗauka a sanadiyyar taka ƙusar. Wannan saƙon da yake barin ƙwaƙwalwa, shi ma a siffar lantarki yake.

Shi kuwa ɓangaren da ke kula da samar da sinadaran “hormones”, yana amfani da kemikals ne wajen tabbatar da sauyi a jikin ɗan adam. Akwai sinadaran “hormones” kala kala a jiki, waɗanda aka kasa su aji-aji.

Su waɗannan sinadarai na “hormones” ana tsarta su ne cikin jinin da ke zagayawa a jikin ɗan adam, domin jinin ya ɗauke su daga wajen da aka tsarta su izuwa inda za su gudanar da aikin da ya kamata su yi.  Akwai masu kula da girman jikin ɗan adam; akwai masu haddasa balaga; akwai masu kula da halayya da ɗabi’ar ɗa namiji ko ‘ya mace; akwai masu kula da narkar da abinci; akwai masu kula da samar da ruwan nono ga mace mai shayarwa; akwai masu daidaita ruwa da gishiri a jiki, da dai sauransu.

Bambanci na biyu tsakanin waɗannan ɓangarori guda biyu shi ne yanayin saurin tasirinsu.

Ɓangaren kulawa da gudanar da jikin ɗan adam, wanda shi ne “Nervous system”, ya na yin aikinsa ne ko tasirinsa yana faruwa ne da sauri; cikin gaggawa. Shi yasa wanda ya taka ƙusa ko wani abu mai tsini ko mai kaifi, za ku ga tayi/yayi saurin ɗauke ƙafarsa/ta; saboda cikin ɗan ƙanƙanin lokaci da bai kai sakwan ɗaya ba, har saƙon lantarki ya bar ƙafar, ya je ƙwaƙwalwa, an fassara shi, an bada umarnin matakin da jiki zai ɗauka a daidai wannan lokaci. Bari in baku misalin yadda saurin wannan saƙo yake: kamar a ce kece ko Kaine za ku kunna fanka ta ceiling, sakwan nawa ake ɗauka kafin fankar ta fara aiki? To shima jikin ɗan adam ya na da irin wannan tsari wajen saurin tafiyar saƙon lantarki.
 
Shi kuwa ɓangaren da ke tsarto da sinadaran “hormones” baya tasiri cikin gaggawa; a hankali yake yin aikinsa. Shi yasa mutum ko kuma ɗan adam yake girma a hankali, cikin tsawon lokaci mai faɗi. Ba rana ɗaya muryar yaro take fashewa ba; kuma ba rana ɗaya mama ke fitowa budurwa ba, kamar yadda ba rana ɗaya gemu ke tsirowa ba. Waɗannan duk misalai ne na rashin gaggawar aiki na wannan sashe mai kula da zubo da sinadarn “hormones” cikin jini.

Na faɗa cewa waɗannan muhimman sassa guda biyu suna aiki tare; zan bayar da misalai.

Yayin da mutum ke yanayin farin ciki, akwai sinadarin “hormone” da ake kira ‘endorphin’ . Shigar wannan sinadari na ‘endorphin’ cikin jini zai iya sanya mutumin ko matar murmushi, nishaɗi da annushuwa. To tun da akwai jijiyoyin motsi (nerves) da suke kula da motsin tsokokin fuska masu motsawa yayin da ɗan adam ke murmushi ko akasin haka, kunga kenan dukka sassan guda biyu da na zayyano suna aiki tare.

Yayin da ɗan adam yaji yunwa, akan tsarto sinadarai da za su fara shirya kayan ciki domin su sa rai da zuwan abinci. Wasu lokutan ko mutum bai ji yunwa ba, idan dai ya yi tunanin abinci a ransa, ko ya yi ido huɗu da abinci, ko yaji ƙanshinsa, to za a fara zubo da waɗannan sinadarai. Hakan zai sa kayan cikin su fara mommotsawa; wato tsukewa da shikawa. Wannan motsi ya na ƙarƙarshin kulawar “nervous system” wato ƙwaƙwalwa, laka, da jijiyoyin da suka taso daga jikinsu.

Sai kaji mutum ya ce /ta ce : “nifa yunwa nake ji, bari in nemi abinci”. To tafiyar nan da za ta yi ko zai yi domin neman abinci, shi ma yana ƙarƙashin umurnin ƙwaƙwalwa da jijiyoyin motsi da suka taso daga jikinta.

Yayin da mutum ya ji tsoro, ana zubo da sinadarin “hormone” da muke kira “adrenaline” ,wanda dunƙulallen kitsen da ke kan ƙoda (adrenal gland) yake samar da shi. Ana tsarta wannan sinadari cikin jini, shi kuma jini zai ɗauke shi ya kaishi izuwa ƙwaƙwalwa. Hakan zai sanya ƙwaƙwalwa ta tura saƙon lantarki izuwa tsokokin jiki na rukuni guda biyu.

Rukunin tsoka na farko za su sanya jiki gujewa abinda ke ba shi tsoro, ma’ana mutum zai take a guje! Saboda haka gungun tsoka da su ke cinyoyi da ƙafafuwa su “nervous system” zai sanya a cikin shiri.

Rukunin tsoka na biyu kuwa, za su sanya jiki cin ɗamara da fafatawa! Saboda haka tsokokin kafaɗa da damtse da hannaye su “nervous system” zai sanya cikin shiri.

Kun ga ni dai yadda abin ya samo asali tun daga lokacin da aka tsarta “hormone” mai suna “adrenaline” cikin jini, har izuwa lokacin da ake shirya tsokar jiki domin tunkara ko guje wa abin tsoron.

’Yan uwa, ku tara a mako mai zuwa da yardar Sarkin Halitta, domin ci gaba da kawo muku bayani akan yadda jikin ɗan adam ke aiki. Kafin nan nake cewa, Allah ya kai mu da rai da lafiya, amin.