Jikin ɗan’adam: Kyakkyawar siffa

Daga MUSTAFA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu Assalamu alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke zaƙulo muku bayanai game da jikin  ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki.

Rubutun yau zai mayar da hankali ne izuwa kyawun siffa da sura ta ɗan adam. Ka tava tambayar kanka/kanki ya akayi wannan sura mai cike da tsari da hikima ke tafiya a doron ƙasa?

A cikin Al-ƙur’ani Mai Girma, Allah Maɗaukakin Sarki ana cewa: ” Haƙiƙa mun halicci ɗan adam a sura mafi kyawun tsayuwa” wannan batu la shakka fihi. Ka taɓa ganin halitta wadda ta fi halittar ɗan adam kyawun zubi da tsari?

Akwai wasu baye-baye da Allah ya yi wa ɗan adam, waɗanda suka bambanta shi da sauran halittu. Yau, za mu kalli wasu muhimman gurare a jikin ɗan adam, da suka banbanta shi da sauran halittu, na gida da na daji.

  1. Ƙwaƙwalwar mutum da yadda take aiki, ya sha ban ban da na sauran halittun Rabbu, saboda tana da sassa na tunani, nazari, hankali, da sanin ya kamata. Bugu da ƙari, ita ce cibiyar tattara bayanai da kuma zartar da hukuncin da ya dace dangane da bayanan da suka shiga cikinta. Ƙwaƙwalwar ɗan adam ce ke kula da narka abinci, bacci, saduwa, fushi ko farin ciki, numfashi, harbawar zuciya, ji, gani, magana, daidaito, da sauransu.

Har yanzu masana jikin ɗan adam ba su san abinda yafi kaso ashirin cikin ɗari ba (20%) na yadda ƙwaƙwalwar bil adama ta ke. Akwai halittun Allah waɗanda ƙwaƙwalwarsu tafi ta ɗan adam girma, amma abin mamaki shi ne, ba su fi ɗan adam zurfin tunani ba. Hasali ma, ɗan adam na iya sarrafa irin waɗannan dabbobi. To shin meye banbancin? Abu ne mai ƙayatarwa: ɗaya daga cikin dalilan shi ne ƙwaƙwalwar mutum na da yawan ƙwayoyin halitta na ƙwaƙwalwa masu tarin yawa fiye da na sauran halittu.

  1. Hannun ɗan adam babbar kadara ce da ta sanya shi kasancewa jagora cikin halittun Ubangiji. Nasan dai ba kowa ne ya san baiwa da hikimar da Allah ya qunshe cikin hannun ɗan adam ba. Kowacce rana, ɗan adam yana amfani da hannunsa wajen motsi mai ‘kaushi’ irinsu tuƙi, ɗaukar jaka, riƙe kofi, sanya tufa, da sauransu. Sannan kuma akwai motsi na musamman wanda hannu ke gudanarwa wanda ke buƙatar cikar nutsuwa misali: rubutu, ko sanya zaren ɗinki cikin ƙofar allura. Ɗan adam yana sarrafa hannunsa wajen yin abubuwa da dama kamar su danna waya, cin abinci, ɗaura ɗankwali, sanya hula, da dai sauransu. Duk waɗannan ayyuka na da kundin bayanai da suka dangance su, taskance cikin ƙwaƙwalwar ɗan adam. Misali: idan akwai salon ɗaurin ɗankwali da kika saba yi mafi yawan lokaci, to haƙiƙa ƙwaƙwalwarki ta yi rajistar dukkan wani lanƙwashe-lanƙwashe da hannunki ke yi domin samar da wannan ɗaurin ɗankwali. Shi yasa da kin tashi yi, za ki ga har kin ɗaura ba tare da yin wani dogon tunani ba.
  2. Akwai ƙafar ɗan adam. Matuƙar mutum ya na da lafiya, to fa ba ya zama waje guda, domin akwai buqatu iri iri da ke sanya ɗan adam ya taka ƙafarsa daga waje izuwa waje. Haƙiƙa ƙafar mutum ta sha ban ban da ta sauran halittu, har masu tafiya a kan ƙafafu biyu. Ita ƙafar ɗan adam, an yi ta ne domin ɗan adam ya iya tafiya a kan tsandauri, wurare masu tudu da kwari, kar har ma tana taimakawa wajen nunƙaya cikin ruwa.

A wannan rubutu, idan nace ƙafa ina nufin abinda ya kama daga idan sawu zuwa yatsun ƙafa. Daga dunduniya zuwa kusan rabin ƙafa, akwai ƙasusuwa 7, daga nan kuma zuwa ƙarshen yatsu, akwai ƙasusuwa 19. Jumulla ƙashi 26 kenan a cikin ƙafar ɗan adam. 
Cikin hikima ta Allah, waɗannan ƙasusuwa ba a jere suke ba, ɗaya na bin ɗaya; sai dai an shirya su ne domin su tangwara, su ɗauki siffa irin ta baka.

Idan za ka ɗora baka a tsaya a kan ƙasa, za ka ga sassa guda biyu (farkonta da ƙarshenta ne kawai ke taɓa ƙasa). Saboda haka, tafin ƙafar ɗan adam shi ma kamar haka yake. Shi ya sa idan ɗan adam zai jarraba kallar sawun kafarsa akan tsandauri bayan ya taka ruwa ko bayan ya yi alwala ko wanka, to zai ga sashen ƙafarsa da bai taɓa ƙasa ba. A Wannan sashe daga cikin ƙafa, akwai ya jerin tantani na (kashe-kara) waɗanda suka yi  siffar igiya da suke tashi daga ƙashi izuwa wani ƙashin. Aikinsu shi ne taimkawa ɗan adam yayin tafiya.

Yanzu bari mu ɗan kalli abinda ke faruwa yayin ɗan adam ke tafiya.  Idan ɗan adam ya taka ƙasa da ƙafar hagu, sai su waɗancan igiyoyin kashe-kara ɗame ko su tamke ta yadda ɗan adam zai sami daidaito a ƙafar, sannan ya jibge nauyinsa a wannan ƙafar na ɗan wani lokaci, sannan ya cilla ƙafar dama gaba domin ya yi taku na biyu. Ita ma haka ne zai faru gareta, za ta ɗauki nauyin jiki na ɗan wani lokaci kafin a taaka ƙafar hagu a Karo na biyu. Wannan shi ne a sauƙaƙe kuma a taqaice yadda ɗan adam ke tafiya.

Amma kamar yadda na faɗa a rubutun da ya shuɗe, mahaɗar ƙashin ƙugu, da ta gwiwa na taimakawa wajen tafiya. Ita mahaɗar ƙashi ta gwiwa, kamar alharga take, wato za a iya buɗe ta, kuma kuma a rufe ta, amma ta fuska ɗaya. Misali, Idan aka ce za a buɗe alharga ta vangaren da yake a kafe (ɓangaren da baya motsi, inda aka kafe alhargar), to sai dai in karya alhargar za a yi. Haka ma mahaɗar gwiwar mutum.

Lokacin da mtum a ke a tsaye kyam, gwiwarsa/ta a kulle ta ke. Saboda haka kafin ɗan adam ya fara motsawa daga wani waje izuwa wani waje, ga yadda abin ke faruwa: ƙoƙon gwiwa zai muskuta gefen waje, shi kuma ƙashin ƙauri wanda yake naniƙe da ƙoƙon gwiwa zai muskuta ciki, ta haka, sai gwiwar mutum ta kulle domin ya samu damar tsayawa kyam.

Amma yayin da yake tafiya, ana buɗe gwiwar ƙafar da ta rabu da ƙasa (a ɗan tanƙwasa ta), sannan a kulle gwiwar da ke kan ƙasa domin ta ɗauki nauyin jiki. Za ku iya gwada tafiya tare da lura da abin da na faɗa anan. Za ku ga hakane. Ta haka ne ɗan adam yake samun yin tafiya ba tare da ya buƙaci wani gwaggwavan taimako daga tsoka ba. Amma fa duk da haka, yayin da ɗan adam ya yi taku ɗaya, an ƙiyasta cewa tsokar nama sama da guda 80 sun motsa.

Dan adam saboda hikimar da Sarkin halittta yayi masa wajen sarrafa hannunsa da ƙafarsa, har wasanni yake gudanarwa irin su kwallon ƙafa, ƙwallon hannu, ƙwallon kwando, tseren mota, tseren gudu da sauransu. 
Ashe idan haka ne, takun ɗan adam shi kansa wani fage ne na gwanintar halittar da Allah Ya yi wa ɗan adam, kuma maudu’i ne da ya kamata a yi rubutu a kai.

Saboda haka ƙwaƙwalwar mutum, hannusa da yadda yake sarrafa shi, ƙafarsa da yadda yake motsa ta, baiwa ce ta Allah babba da aka keɓe waɗannan sassa da su na jikin ɗan adam.

Masu karatu mu haɗu mako mai zuwa idan Allah ya kai mu, domin ci gaba daga inda na tsaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *