Jiran zantawar El-Rufai ta biyu

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Duk wanda ya daɗe masu azancin magana suka ce zai ga daɗau. A ’yan shekarun nan, ba zan iya tuna babban taron wata jam’iyya da ya ɗauki hankalin jama’a irin na APC ba. Wato wannan babban taro inda gwamnan Jihar Yobe wanda ke jagorantar kwamitin shirya taron zai miƙa ragama ga sabon shugaban da za a zaɓa ko daidaitawa a ɗora kan shugabancin jam’iyyar.

Ba mamaki dage gudanar da taron a baya kimanin sau biyu ko ma fiye da haka ya ƙara jan hankalin jama’a kan dalilan ɗaukar matakan. Tun bayan da majalisar ƙoli ta jam’iyyar ƙarƙashin shugaba Muhammadu Buhari ta sauke tsohon shugaban jam’iyyar Adams Oshimhole da sauran masu muƙamai; a ka damka ragamar jam’iyyar ga Mai Mala Buni wanda dama shi ne tsohon sakataren jam’iyyar.

Mafi ɗaukar hankalin abin da ya faru shi ne zantawar da gwamnan Kaduna Nasir El-rufai ya yi a gidan talabijin na CHANNLES inda ya ke cewa bisa umurnin shugaba Buhari sun ɗauki matakan kawar da Mai Mala daga kujerar da naɗa gwamnan Neja Abubakar Sani Lolo ya cigaba da gudanar da lamuran jam’iyyar zuwa lokacin babban taro. Elrufai ya ba da tabbacin cewa sai dai gwamna Buni ya dawo Nijeriya daga jinyar da ta kai shi Daular Larabawa a matsayin gwamnan Yobe amma ba jagoran APC ba.

Haƙiƙa daga nan a ka fahimci kan gwamnonin APC ya rabu gida biyu. Hakan ya ƙara fitowa a fili bayan shi kuma gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma ya shiga gidan talabijin ɗin na CHANNLES ya na nuna ba wanda ya kwaɓe Buni daga kujerarsa kuma su na mara ma sa baya don kammala aikin shirya taro.

Ko lokacin da gwamnan Neja Abubakar Sani ya shiga helkwatar jam’iyayr bai yi wani bayani mai gamsarwa na cewa shi ne sabon shugaba ba. Abin da ya ɗan nuna akwai rina a kaba shi ne inda a ka tambaye shi ko ina Buni, ya amsa da bai sani ba. Ga shi yanzu gwamna Buni ya dawo ya amshi ragamar aikin sa daga hannun gwamnan Neja ya na mai cewa dama riƙo ya ba shi.

Tun da tabbata Buni ya dawo kan kujera, sai a ka yi tsammanin ganin gwamna Nasir El-rufai a gidan talabijin ya na mai cewa bai yarda da mulkin Buni ba, ko kuma aƙalla ya ce an sulhunta ne ya sa Buni ya kai labari. Har an doshi gudanar da babban taron ba amo babu bayani daga Elrufai. Irin waɗannan kalaman a kafar labaru na da irin na sa sammates ɗin. Idan an furta kalamai musamman daga ɓangaren shugabanni ko mutane masu tinƙaho ’yan gar-da-gar ne wajen fadar magana, za a so ganin gaskiyar sakamakon zancen. In kuma bai tabbata ba ko an sauya matsaya sai a fito a yi bayani filla-filla cewa ga fa abin da ya faru.

Masu sharhin siyasa sun aza alhakin dambarwar APC kan masu faxi-tashin neman samun tikitin takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar. Gaba ɗaya manuniyar APC ta nuna ɗan takarar shugaba a jam’iyyar daga kudu zai fito, don haka gwagwarmayar neman mataimaki ya zama tsakanin gwamnonin arewa.

Gaskiya zai yi wuya a ce akwai gwamnna da ba ya so a ɗauke shi ya zama mataimakin shugaban ƙasa, inda daga bisani ya na da tagomashin hawa babbar kujerar. Saboda dalilan logar siyasa, gwamnonin ba za su furta a fili ko amsa tambaya kan neman mataimakin shugaba ba.

Ƙarƙari gwamna mai ƙoƙari ya ce ma ka ai ba a zo wajen ba, sai a jira sai an kammala babban taro in ya so shugabannin jam’iyya za su zauna su duba abin da ya dace. Lamarin tamkar siyasa ne a cikin siyasa. Kowane ɓangare na ƙoƙarin yin dabarun samun mafita ko samun wajen zama mai inganci a 2023 bayan shugaba Buhari ya kammala wa’adi.

Akasarin ’yan siyasar Nijeriya na da burin girma daga ƙaramar hukumar zuwa jihar, daga jihar zuwa tarayya daga taraiya zuwa masu naɗa shugabanni ko wucewa majalisar ɗinkin duniya da sauran hukumomin ƙasa da ƙasa. Abin da ya fi zama al’adar ’yan siyasa a Nijeriya shi ne maƙalewa kan madafun iko da bin kowace irin dabara wajen zama kan muƙamai har sai rai ya yi halinsa nan kuma ba sauran dabara. Wani abu kuma shi ne rashin ganin laifin kai da bin kowace hanya wajen nuna a kan gaskiya a ke ko da kuwa an san cewa an zarme.

Daidai lokacin da gwamna Bello ya shiga helkwatar APC yayin da gwamna Buni ya ke ƙetare neman magani, an yayata cewa shugaba Buhari ya ba da umurnin tsige Buni daga kujera. Duk da ba a yi taron majalisar ƙoli ba, kuma ba saƙon sauti ban a rubutu, sai hakan ya kawo ruɗani inda wasu su ka ce amince da raɗe-raɗin wasu kuma su na tababa don nan take jami’an jam’iyya su ka ce sam ba wani sauyin shugabanci da a ka samu. Za su iya dogara ga cewa ba su samu takarda ko faruwar hakan a taron majalisar ƙoli. Ko ma me za a ce ruwa ba ya tsami banza.

Akwai dai abin da ya faru da ba mamaki mantawa da cewa akwai dokoki ko hanyar cire shugaban jam’iyya da ba a bi ba ya sa mayar da wuƙa kube. Wata majiyar kuma ta nuna wasu da ke tare da gwamna Buni sun taka rawa wajen kawar da yunƙurin juyin mulki da a ka yi ma sa. In an samu irin wannan dambarwa to a ƙarshe zai zama ko ɓangare daya ya samu galabar ɗaya ɓangaren ya bi ko ba ya so, ko kuma ya zama duk ɓangarorin biyu su rasa cimma muradun da su ka tsara a haɗu a tsakiya. Zuwa bayan taron za a ƙara fahimtar ɓangaren da ya yi galabar ko kuma an samu canjaras ko kuma an samu yanayin da babu gara ba daɗi.

Shugaban kwamitin shirya babban taron APC na zaɓen sabbin shugabanni Mai Mala Buni ya ce sun kammala dukkan shirye-shirye don gudanar da babban taron jam’iyyar. Mai Mala Buni na amsa tambaya ne kan halin da a ke ciki a jam’iyyar bayan tabbatar da kwamitocin shirya taron.

Gwamna Buni wanda ya ce ba wata baraka a jam’iyyar a halin yanzu kuma shi a iya matsayarsa ba a samu wata tangarɗa ba kan shugabancinsa yayin da ya fita ƙetare don dama riqo ya ba wa gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello. Game da yadda a ka samu gwamna Elrufai ya ce shugaba Buhari ya ba da umurnin kawar da shi daga jagoranci, inda nan take gwamna Hope Uzodinma ya ce ba haka ba ne, gwamna Buni ya ce ya yi taro da dukkan gwamnonin don haka ba ma batun wani ɓangare.

Wani abu mai ɗaukar hankali a jam’iyyar shi ne cigaba da takarar wasu da ke waje da yankin arewa ta tsakiya da jam’iyyar ta warewa kujerar shugaba, misali tsohon gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari da ke arewa maso yamma da ke takarar.

Tsohon gwamnan Borno Sanata Ali Sheriff daga arewa maso gavar ya miƙa wuya ga tsarin jam’iyyar da ma shugaba Buhari inda ya janye daga takarar.

Har yanzu a na batun raɗe-raɗi ne na cewa Sanata Abdullahi Adamu daga Nasarawa ne zai zama sabon shugaban, don ’yan yankin na arewa ta tsakiya na cikin takarar. Mustapha Salihu daga Kwara ya ce bai yi mamakin yadda lamura ke gudana ba, don hakan ma tsarin dimokraɗiyya ne.

Karsashin gudanar da babban taron APC mai mulki a Nijeriya ya ragu don rashin gagarumar gasa tsakanin manyan ’yan takara. Duk da dai ga manyan allunan hotunan ’yan takara musamman na yankin arewa ta tsakiya, amma ba shige-da-fice na kamfen a zahiri da hakan bai rasa nasaba da raɗe-raɗin tuni an san wanda zai zama sabon shugaban.

A na sa ran fiye da wakilai 4000 za su halarci taron da za a gudanar a dandalin taruka na EAGLE da ke tsakiyar Abuja.

A daf da ranar taron, ba mamaki a datse titunan tsakiyar birnin don samar da tsaro inda ya zama wajibi masu motoci su riƙa zaɓar wasu titunan gefe-gefe har sai an buɗe tsakiyar garin.

Rahotanni sun tabbatar da kame ɗakunan masaukan baƙi don sauke wakilan jam’iyyar da za su zo daga jihohin ƙasar 36 da kuma masu masaukin baƙi wato Abuja.

Duk abin da ya zama darasin da a ke muhawara a kai shi ne taron nan ne zai zama zakaran gwajin dafin tasiri ko akasin haka da APC za ta yi a babban zaɓen ƙasa mai zuwa a watan febrerun baɗi. Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta samu shekaru 16 kan karaga inda yanzu APC ta ke ƙoƙarin kammala shekaru 8 da buƙatar zarcewa kan mulki.

A gefe guda waɗanda su ka gaji da tsarin manyan jam’iyyun biyu na yunƙurin kafa wata gagarumar jam’iyya da za ta nemi ture biyun. Jam’iyyu a Nijeriya kan zama dandamalin da ’yan siyasa ke hawa ne don samun muƙaman gwamnati amma ba lalle ’yan siyasar na amfani da manufofin jam’iyya don gudanar da lamuran su ba. Wannan a fili ya ke don za ka ga a dalili na cimma muradin kashin kai babban mai riƙe da kujerar siyasa kamar gwamna ya yi wuf ya sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya ya na mazurai wai an yi ma sa laifi ne.