Saɓanin rahotanni dake yawo a kafar sadarwa cewa jirgi mai saukar angulu ya faɗi a kaduna, rundunar sojojin Najeriya sunce jirgi marar matuƙi ne ya faɗi.
Lamarin ya auku ne a wani ƙauye da ake kira Rumji wanda yake kilomita 12 daga sansanin sojojin.
Don haka mutane su guji, yaɗa jita jita har sai sun tabbatar inji Edward Gabkwet, jami’in yaɗa labarai na rundunar. Yanzu haka an fara bincike a san dalilin faruwar wannan lamarin.