Jirgin Abuja-Kaduna: Za a hana yin waya a jirgin ƙasa

*An soke zirga-zirgar dare
*Akwai tsare-tsare na sarari da ɓoye – Ministan Sufuri
*Za a ƙara kuɗin tikiti da albashin ma’aikata, inji Ministan Sufuri
*Ni da iyalina za mu riƙa hawa jirgin saboda tabbacin tsaronsa, inji Ministan Ruwa
*Mu na aiki kan samar sababbin manufofi – Shugaban Hukumar Daraktoci

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa, akwai yiwuwar ta hana amfani da waya a cikin jiragen ƙasan Abuja zuwa Kaduna, wanda aka dakatar da zirga-zirgarsu tun bayan harin da aka kai wa jirgin fasinjojin a cikin watan Maris da ya gabata.

Shugaban Hukumar Daraktoci na Kamfanin Sufurin Jiragen Ƙasa na Nijeriya, Alhaji Ibrahim Hassan Musa, ne ya shaida wa Blueprint Manhaja a yayin tattaunawarsa da mu kan yunqurin dawo da sufurin jiragen a tsakanin Abuja zuwa Kaduna da ake yi kwanan nan.

Ya ce, Hukumar Daraktocin ta na nan tana tsara manufofi, waɗanda za su taimaka wajen ganin an inganta tsaro da kuma sufurin jiragen, don kiyaye abinda ya faru a baya na harin da aka kai masa.

“Wannan abu ne na kowa da kowa tun daga Gwamnatin Tarayya zuwa Ma’aikatar Sufuri zuwa jami’an tsaro da ma shi kansa Kamfanin Sufurin Jiragen Ƙasan da ma ’yan Nijeriya bakiɗaya, kamar yadda minista ya faɗa. Don haka mu ma a ɓangaren Hukumar Daraktocin kamfanin mu na yin iyaka ƙoƙarin na ganin mun bayar da goyon baya da taimakon da ya dace, don ganin ɓangaren gudanarwa na kamfanin ya samu nasarar kare rayukan ’yan ƙasa,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, “Mu na da niyyar idan an hau jirgi za a riƙa kashe waya. Yawan wayoyin da mutane ke yi, a taƙaita, saboda sadarwa. Yanzu idan ka je banki, ana barin ka ka yi waya? Ba a bari! Saboda me? Saboda tsaro. Ka gani a cikin jirgin sama ma ko kaso ka yi, ba a yi.”

A nasa ɓangaren, Ministan Sufuri na Nijeriya, Alhaji Mu’azu Jaji Sambo, a tattaunawarsa da Blueprint Manhaja lokacin gwajin jirgin da ya yi tsakanin Abuja zuwa Kaduna tare da manema labarai ranar Lahadin da ta gabata, ya ce, an soke zirga-zirgar jirgin da daddare.

Ya ce, “a halin yanzu dai za mu dai za mu tabbatar da cewa, jirgi ya daina aiki ƙarfe 5:00 na yamma.”

Kan batun farashin tikitin jirgi kuwa ya ce, “Batun farashin tikitin jirgi, mu na tunanin ƙarawa gaskiya… Za mu ƙara farshin jirgin ne, saboda abubuwa sun tashi yanzu.”

Daga sai ya tabbatar da cewa, akwai shiri kan gyara albashin ma’aikatan kamfanin, inda ya ce, “Mun samu ‘approval’ na gyara albashinsu.”

Shi kuwa Ministan Ruwa, Alhaji Sulaiman Adamu, wanda ya yi wa Ministan Sufurin rakiya zuwa Kadunan, ya shaida wa Blueprint Manhaja gamsuwarsa ga shirin da aka yi na dawo da zirga-zirgar jirgin, yana mai cewa, “Ana bude jirgin nan ma, iyalina za su fara zuwa Abuja, kuma ni ma duk sanda zan samu zuwa Kaduna, ni ma zan shigo in sha Allah.”

Ya ƙara da cewa, “Tabbas na gamsu. Da ma shi minista saboda ya san ni mazaunin Kaduna ne, wanda kuma muke aiki tare da shi, sai ya gayyace na zo na taya shi duba aikin jirgin kuma a bada shawara da gudunmawa.

“Kuma alhamdulillahi na ga tsari. Tsari ya yi kyau, kuma hankalina ya kwanta. Kuma da ma ɗaya daga cikin abin shine, don jama’a su ma su gani. Don haka hankalinmu ya kwanta, mun gamsu da abinda muka gani.”

Lambar ’Yan Ƙasa:

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da samar da tsarin yin amfani da Lambar ‘Yan Ƙasa (NIN) ga kowane fasinja dake sha’awar hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna.

Ministan Sufuri na Nijeriya, Mu’azu Jaji Sambo, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi lokacin da ya ke zagayawa da ‘yan jarida, ciki har da Blueprint Manhaja, don duba irin shirye-shiryen da aka yi, don dawo da zirga-zirgar, wacce aka dakatar da ita ranar 28 ga Maris, 2022, sakamakon harin ta’addanci da aka kai masa har aka kashe wasu fasinjoji kuma aka yi awon gaba da wasu.

Ministan ya ƙara da cewa, a cikin makon nan da ake shiga ne za a fara sayar da tikitin jirgin makonni bayan sako dukkan fasinjojin da aka yi garkuwa da su.

“Hawa jirgi gaba-gaɗi”

Ministan Sufurin Nijeriya, Mu’azu Jaji Sambo, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya masu sha’awar hawa jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna da su yi shirin hawa gaba-gaɗi ba tare da wata fargaba ba, yana mai cewa, an yi kyakkyawan tanadi, don kare rayuka da lafiyar fasinjoji a yayin da zirga-zirgar jingin ta dawo.

Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Lahadi, ciki har da Blueprint Manhaja, yayin duba irin shirin da Gwamnatin Tarayya ta yi na sake buɗe zirga-zirgar jiragen ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna.

“Ina so na tabbatar wa duk wanda zai shiga jirgin nan, wallahi ya shiga jirgin nan kai-tsaye ba tare da wata tantama ba,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, akwai tsare-tsare na tsaro waɗanda suke a fili da na ɓoye. Don haka babu sauran fargabar tsaro a jirgin.

A yayin da yake bayar da tabbacin tanadin tsaron da aka yi wa zirga-zirgar jirgin, don rayukan fasinjojinsa, ya ce, “alhamdulillahi, tunda ka gan mu a nan, ka san cewa, mun yi iya abinda ɗan adam zai iya yi. Sai mu cigaba da roƙon Allah Ya ƙara tsare mu, Allah Ya tsare ƙasarmu, Allah Ya ba mu sa’a mu miƙa mulki shekara mai zuwa lafiya.”

Lokacin da ya ke amsa tambaya kan tanadin da aka yi na shiga jirgin, ya ce, yanzu sai da Lambar ‘Yan Ƙasa za a riƙa sayen tikiti.

Don haka ya yi ƙarin haske kan batun ‘yan ƙasar waje, waɗanda ba su da lambar, sai ya ce, “Bari na gaya maka wani abu ɗaya… Yawancin waɗanda suke da hannu a irin waɗannan tashe-tashen hankulan, ai ‘yan ƙasashen waje ne,” inji Sambo.

Sai dai a cigaba da tattaunawar ya ƙara da cewa, Hukumar Kula da Jiragen Ƙasa ta Nijeriya ta yi haɗin gwiwa da Hukumar Rijistar ‘Yan Ƙasa, wacce ta ke da tanadi na yi wa ‘yan ƙasashen waje rijistar wucingadi a lokacin zamansu cikin Nijeriya, yana mai cewa, hukumar za ta buɗe ƙananan ofisoshinta a tashoshin jiragen ƙasa na Abuja da Kaduna, don tabbatar da aikin tantance fasinjojin ya tafi daidai.

A ƙarshe, Minista Sambo ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin tsaronsu a cikin jiragen.

Jinkiri

Gwamnatin Tarayya ta sanar da jinkirta dawo da zirga-zirgar jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja da ta ayyana yi a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a ranar Lahadi.

Ministan ya mayarwa da ’yan Nijeriya murnarsu ciki yayin rangadin da ya kai kan layin dogon da ke Kaduna domin tabbatar da matakin shirye-shiryen da aka kammala gabanin dawo da jigilar.

Ministan wanda bai fayyace ainihin ranar da za a dawo da jigilar ba, ya ce jinkirin da za a fuskanta ba zai wuce na tsawon mako guda ba.

A cewar ministan, “Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da wani sabon tsarin siyan tikitin jirgin, wanda a cewarsa shi ne mafarin binciken tabbatar da tsaro wanda zai ba mu damar tantance waɗanda ke hawa jirgin a kowane lokaci.”

A makon da muka yi bankwana da shi ne Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 28 ga watan Nuwamban 2022, a matsayin ranar da za a dawo da aikin jirgin ƙasan da ke zirga-zirga tsakanin Kaduna da Abuja, babban birnin ƙasar.