Jirgin Nigeria Air da aka ƙaddamar na haya ne, cewar Shugaban Kamfani

Daga WAKILINMU

Shugaban kamfanin Nigeria Air, Captain Dayo Olumide, ya bayyana cewa jirgin kamfanin da aka ƙaddamar kwanaki kaɗa kafin ƙarewar wa’adin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, hayarsa aka yi daga ƙasar Habasha domin nuna wa ‘yan Nijeriya.

Olumide ya bayyana haka ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin sufurin jiragen sama.

Ya ƙara da cewa, muddin jirgin mallakar Nijeriya ne, ya zama dole a yi wa jirgin rijista da sunan Nijeriya.

Yayin da ya rage wa gwamnatin Muhammadu Buhari kimani sa’o’i 72, aka ga gwamati ta shigo da jirgin wanda ya sauka a Babban Filin JIrgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

A jawabinsa a wajen taron ƙaddamar da jirgin, tsohon Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya ce haɗin gwiwa da kamfanin jiragen sama na Habasha (ET) wanda ya fi son sayen jiragen Nijeriya Air, zai haɗa kasuwannin ƙasashen biyu.

Ya ce, “Wannan shi ne abu ɗaya da aka rasa daga kayayyakin more rayuwa a harkokin sufurin jiragen sama a ƙasar.

“Kamfanin jirgin sama wanda ya yi daidai da girman yanayin kasuwa a Nijeriya saboda yanayin ƙasa da arzikinsa, lallai muna buƙatar irin kayayyakin more rayuwa da muke samu a yau da sunan Nigeria Air Limited,” in ji Sirika.

Haka nan, ya ce, “An fuskanci ƙalubale amma ba mu bari sun karkatar mana da hankali ba inda a yau muka tsinci kanmu a wannan matsayi. Muna fatan hakan ya amfani ƙasarmu, al’ummarta, makomarta da ma bil’adama.”

Sai dai kuma, bayanan da Shugaban kamfanin Nigeria Aire ya yi a ranar Talata, sun ci karo da na tsohon Minista Sirika, inda aka ji shi yana cewa jirgin da aka ƙaddamar ba shi da rijista.

Ya ci gaba da cewa, an shigo da shi ne daga ƙasar Habasha bayan samun izini da ‘yan kwanaki sannan aka mayar da shi bayan kammala abin za a yi.

Da yake amsa tambayar Kwamitin, Olumide ya ce “Jirgin da ya shigo (Nijeriya) ya koma, ta halastacciyar hanya aka ɗauki hayarsa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *