Jirgin sama zai yi feshin maganin ƙwari a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Babban sakatare a ma’aikatar aikin noma ta Jihar Katsina Alhaji Aminu Waziri ya ƙaddamar da fara shirin feshin maganin ƙwari ta hanyar amfani da jirgin sama a rabar Laraba.

A farkon makon da mu ke ciki ne ma’aikatar kula da harkokin noma ta Nijeriya a cikin wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewar za ta yi amfani da jirgin sama don yin feshin maganin ƙwari a Jihar Katsina.

“Ma’aikatar aikin noma a ƙarƙashin shirin yaƙi da ƙwari masu varnata kayan amfanin gona za ta yi amfani da jirgin sama don yin feshin maganin ƙwari da su ka haɗa da farin ɗango da dai sauran ƙwari masu kassara amfanin gona a Jihar Katsina,” inji sanarwar.

Feshin wanda aka ƙaddamar da shi ranar Laraba za a kwashe kimanin kwanaki biyar ana aiwatar da shi a sassan jihar daban-daban.

A cewar wani manomi Malam Hashimu Ahmad da ya zanta da Manhaja a Katsina jim kaɗan bayan ƙaddamar da shirin, ya bayyana cewar feshin zai taimaka wajen daƙile varnar da ƙwarin ke haifarwa akan amfanin gona a duk shekara gami da haɓaka aikin noma idan aka yi la’akari da yadda ƙwarin ke haddasa wa manoma hasara a duk shekara.