Jirgin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima ya sauka Borno

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Maiduguri

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu tare da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima da wasu gwamnoni biyar sun yi wa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno tsinke domin gudanar da yaƙin neman zaɓe.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, da takwarorinsa na jihohin Yobe da Gombe, haɗi da jiga-jigan gwamnatin Jihar Borno, su ne tarbi tawagar ɗan takarar da ƙusoshin Jam’iyyar APC yayin gangin da ya gudana ran Asabar.

Jim kaɗan da saukarsa a Maiduguri, Tinubu da jiga-jigan jam’iyyar APC suka shiga tattaunawa ta musamman da masu ruwa da tsaki a babban ɗakin taro na Multi-Purpose Hall da ke Gidan Gwamnatin jihar a Maiduguri, kafin zuwa filin da za a gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓen.

Bugu da ƙari, tawagar ta kai ziyarar ban-girma a Fadar Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai, kafin zuwa filin wasa na El-kanemi Warriors inda a nan aka shirya gudanar da taron.

Wurin taro

Gwamnonin da suka halarci gangamin sun haɗa da Mai Mala Buni na Yobe, Dr. Abdullahi Ganduje na Kano, sai Inuwa Yahaya na Jihar Gombe tare da Engr. Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa.

Al’ummar Jihar Borno sun yi wa manyan baƙin gagarumar tarba, yayin da jama’a suka mamaye tatin da ya shiga zuwa Fadar Shehun Borno tare da ɗaga wa tawagar manyan baƙin hannu, sannan a gefe ɗaya mawaƙi Rarara ya nishaɗantar da taro da waƙoƙin siyasa.