Jiri ya kwashi Shugaban Ƙasar Zambiya ya yanke jiki ya faɗi a taro

Daga AISHA ASAS

Shugaban Ƙasar Zambiya, Edgar Lungu, ya yanke jiki ya faɗi a wajen wani babban taro na ƙasar da aka gudanar a Lahadin da ta gabata a Lusaka, babban birnin ƙasar.

Jim kaɗan bayan faruwar lamarin, sakataren gwamnatin ƙasar, Dr Simon Miti, ya bayyana wa manema labarai cewa Shugaba Lungu ya wattsake har ma ya ci gaba da harkokinsa.

Dr Miti ya ce jiri ne ya kwashi shugaban yayin da yake jawabi a wajen taron bikin Ranar Tunawa da Dakarun Ƙasar karo na 46 inda ya yanke jiki ya faɗi, amma cewa ya wattsake ba tare da jimawa ba.

Bayanai sun nuna da kansa Mr Lungu ya taka ya je ya shiga motarsa sannan ya koma Fadar Shugaban Ƙasa.

Binciken Manhaja ya gano cewa ko a 2015, shugaban ya fuskanci irin wannan matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *