Jirigin ƙasan Abuja-Kaduna: A gaggauta sako mana ’yan uwanmu, inji dangin waɗanda aka sace

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Iyalai da dangin waɗanda ’yan bindiga su ka sace a hanyar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna sun bayyana damuwarsu akan irin halin da ’yan uwansu ke ciki a hannun masu garkuwar, inda suka ce a gaggauta a sako su. Sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da suka fitar cikin makon nan.

Sanarwar ta ce, “a jiya, mun sami labari mai firgitarwa daga waɗanda suka sace fasinjojin jirgin Ak9 da suka taso daga Abuja ranar 28 ga Maris, 2022 da qarfe 6:10 na yamma zuwa Kaduna amma ba su kai ga inda aka nufa ba.”

Sanarwar ta qara da cewa, “mu dangi ne. Nijeriya babbar ƙasa ɗaya ce, Afirka babban nahiya ɗaya ce, duk duniya kowa daga tsatson Adamu da Hauwa’u ya fito. Ya kamata mu riƙa nuna wa junanmu ’yan uwan taka.”

“Wataƙila ba za mu yi tarayya da suna ɗaya, addini, ƙabila, al’umma, harshe ko launin fata ba amma muna raba ainihin abin da ya sa mu duka ɗaya, wato ’yan adam. Ba wani ɗan adam da aka yi daban da sauran. Daga cikin ciki har zuwa mutuwa, dukkanmu muna zaren juyin halitta iri ɗaya.

“A jiya ne muka samu labari ta kafar yaɗa labarai cewa, masu garkuwa da mutanen da suka sace mana ’ya’yanmu don a sako ’ya’yansu da iyayensu da gwamnati ta kama,” inji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “wace duniya ce wannan? Wannan wace irin cin amana ce? Ina halayyar ɗan Adam a cikin wannan? Kamar duk mutanen duniya sun manta da batun amma mu garemu har yanzu muna rayuwa a ranar 28 ga Maris ne. Wataƙila kwanaki sun shuɗe amma ba mu yi ba.”

“Shin waɗannan munanan halaye za su kai mu ga cigaba kuwa?, kuma ina tambayarku yanzu, me ku ke tunanin makomarsu za ta kasance a gaba? Kwanaki 7 har sai mun kasa cewa muna da tsarin da ke aiki ga talakawa.

A kwanaki 7, ya kamata mu yi tsammanin jana’izar ko murna? Kwana 7 iyaye su rungumi ‘ya’yansu ko su yi kuka?, Cikin kwanaki 7 wasu matan su yi kwalliya ko su yi zaman takaba? kwanan 7 kafin ’yan bindiga da ta’addanci su yi nasara, kwanan 7 kaɗai ya rage.

“Muna kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, hafsoshin tsaro, shugabannin hukumomin tsaro, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama na ƙasa da ƙasa da su ceto iyalanmu. Su ma mutanen su ne. Ba za a iya yin sulhu ba tare da tattaunawa ba. Kada ku rufe babin labarinmu, zai canja tarihi har abada. Ku saki ‘ya’yansu mu dawo da danginmu, da danginku. Kar ku rufe ido kan halin da muke ciki,” inji sanarwar.

Daga ƙarshe snaarwar ta ce, “muna kuma kira ga dukkan masu neman shugabancin Nijeriya a yau. Wannan ba lokaci ba ne don yin son kai tare da ra’ayoyinku da tsare-tsarenku, Ku tabbatar da alƙawuranku da yaqin neman zaɓe na gaskiya. Muna kuma ƙara kira ga mai girma shugaban ƙasarmu kuma kwamandan rundunar sojojin tarayyar Nijeriya da ya yi la’akari da kuma bijirewa buƙatar masu garkuwa da ‘yan uwa da kuɓutar da ‘yan Nijeriya da ‘yan ƙasarsa da ba su ji ba ba su gani ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *