Jonathan ya ƙaddamar da hanya a Bauchi

Daga AISHA ASAS

A Talatar da ta gabata Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ƙaddamar da babbar hanya ta farko wadda Gwamna Bala Mohammed ya gina a Bauchi.

Hanyar wadda ta haɗa garin Sabon Ƙaura da ƙauyen Miri, na daga cikin hanyoyin farko-farko da gwamnan ya bada aikinsu a kwanaki 100 na farko da ya yi a kan mulki.

Sa’ilin da yake jawabi yayin bikin ƙaddamarwar, Gwamna Bala ya ce sabuwar hanyar da aka gina mai nisan kilomita 6.2, an bada kwangilar ne kan kuɗi Naira bilyan N2.

Daga nan, ya yaba wa Jonathan bisa ɗora shi kan hanya mai ɓulewa a siyasance tare da sanar da shi dabarun shugabanci nagari.

Bala ya ce kawo yanzu, gwamnatinsa ta bada kwangilar hanyoyi a karkara da birane na tsawon kilomita 100. Tare da cewa ya ɗauki matakin aiwatar da ayyukan ne duba da yadda ya zo ya cim ma ababen more rayuwa a jihar sun taɓarɓare.

A nasa jawabin, Jonathan ya nuna farin cikinsa da godiyarsa ga Gwamna Bala bisa gayyatar sa da ya yi don ƙaddamar da hanyar wadda aka sanya mata sunansa.

Haka nan, Jonathan ya sake yaba wa Bala kan yadda bai yarda ya yi watsi da shi ba saɓanin wasu ‘yan siyasar wanda tuni suka yi hannun riga da ubannin gidansu.

Kazalika, ya yi godiya ga Sarkin Bauchi, Rilwanu Suleiman Adamu, game da muƙamin da ya ba shi a matsayin ‘Jigon Bauchi’.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *