Jonathan ya yi watsi da fom ɗin da aka saya masa na takarar APC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon shugaban ƙasar Nijeriya, Goodluck Jonathan ya nesanta kansa da fom ɗin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC da wata ƙungiya ta saya masa, inda ya yi watsi da batun tsayawa takara a babban zaɓen 2023.

A wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran tsohohon shugaban ƙasar ta fitar sa’o’i kaɗan bayan ƙungiyar ta sayi fom ɗin a kan Naira miliyan 100, Jonathan ya bayyana kyamarsa ga matakin, yana mai jaddada cewa shi ba ɗan jam’iyyar APC ba ne.

“Saboda haka ana kira ga jama’a da su yi watsi da abin da ƙungiyar ta aikata, domin ba da sanin Dakta Goodluck Jonathan ko izininsa ta yi ba,” inji sanarwar.

A ranar Litinin da yamma ne dai wata baƙuwar ƙungiya mai suna ‘Ƙungiyar Fulani’ ta saya wa tsohon Shugaban Ƙasar fom ɗin, duk da cewa bai taɓa bayyana cewa ya koma jam’iyyar APC ba.

Jim kaɗan bayan nan ne ofishinsa na yaɗa labarai ya sanar cewa, “tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya samu labarin wata ƙungiya mai suna ‘Fulani Group’ ta sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC da sunansa.

“Muna sanar da jama’a, musamman al’ummar Nijeriya cewa Dokta Goodluck Jonathan ba shi da masaniya ko wata alaƙa da sayen fom ɗin da aka yi da sunansa, hasali ma ba shi da kowace irin alaƙa da ƙungiyar.

Duk da haka sanarwar ta bayyana godiyar Jonathan ga ’yan Nijeriya da ke ta kiraye-kirayen ya fito takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023 da ke ƙara matsowa.

Amma ofishin ya ce, “muna ƙara jaddada cewa a halin yanzu ba shi da aniyar karɓar wannan tayin da ake yi mishi, duk da cewa akwai masu ganin cewa fitowar tasa ita ce kishin ƙasa.”