Fitaccen ɗan damben ‘boxing’ ajin masu nauyi, Anthony Joshua ɗan Ingila, ya yi watsi da rahotannin cewa ya amince da yarjejeniyar karɓar kuɗi fam miliyan 15 kwatankwacin Yuro miliyan 18 don janyewa daga shirin sake karawa da Oleksandr Usyk na ƙasar Ukraine.
A watan Satumban shekarar bara ne dai Usyk ya kwace dukkanin kambun Joshua na WBA da IBF da kuma WBO, bayan lallasa Joshua ɗin da yayi a fafatawar da suka yi.
Rashin nasarar da Joshua ya yi a karon battarsa da Oleksandr Usyk, ita ce karo na biyu da fitaccen dan damben boxing ɗin ya fuskanta tun bayan ficen da yayi.
A baya bayan nan ne kuma kafafen yaɗa labarai da dama ciki har da na ƙasar Birtaniya suka wallafa rahoton cewa, Joshua ya yarda Usyk ya biya fam miliyan 15, domin janyewa da shirin sake fafatawar da aka tsar za su yi, labarin da fitaccen ɗan damben ɗan asalin Nijeriya ya bayyana a matsayin mara tushe.
A ƙarshen watan Satumban da ya gabata, fitaccen ɗan damben boxing na Ingila ya kafe kan cewa zai iya fafatawa da Tyson Fury wani fitaccen ɗan damben na boxing wani lokaci nan gaba kaɗan, koda kuwa ba tare da kambunansa guda uku na duniya ba.