Juyin mulki: Nijeriya na neman ɗan ƙasar Birtaniya ruwa a jallo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Nijeriya ta ayyana wani ɗan ƙasar Birtaniya, Andrew Wynne (Andrew Povich ko Drew Povey), a matsayin wanda take nema ruwa a jallo kan yunƙurin kifar da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Rundunar ’yan Sandan Nijeriya ta ce tana gudanar da bincike na musamman kan yadda sojojin sa-kai daga ƙasar waje suke shiga ƙasar suna neman hamɓarar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin dimokuraɗiyya.

Mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya sanar a ranar Litinin cewa hujjojin da kuma bayanan da suka samu daga Andrew Wynne sun tabbatar da hannunsa a yunƙurin kifar da gwamnatin Nijeriya.

Adejobi ya bayyana cewa Andrew Wynne ya bayar da tallafin kuɗaɗe da kuma tsare-tsare zanga-zangar da aka gudanar kan tsadar rayuwa da nufin amfani da zanga-zangar wajen  ganin an hamɓarar da gwamnaitin Nijeriya.

Bugu da ƙari ɗan ƙasar na Birtaniya ne ya ba da umarni tare da sanya ido kan zanga-zangar yunwar da aka gudanar a faɗin ƙasar a watan Agusta.

Jami’in ya ce binciken rundunar ya gano cewa Andrew Wynne yana zaman haya ne a gidan Labour House da ke Abuja.

Adejobi, ya ci gaba da cewa Andrew Wynne ya kama wurin haya ne da sunan buɗe shagon sayar da litattafai mai suna ‘Iɓa ɓalley Bookshop’.

Sannan kuma shi ne ya assasa makarantar ‘STARS of Nations Schools’ domin ɓatar da sawu game da manufarsa.