Sojojin da suka yi juyin mulki a ƙasar Gabon sun sanar cewa Kanal Brice Clotaire Oligui Nguema ne sabon shugaban ƙasar wanda hakan ya kawo ƙarshen mulki na shekara 55 da zuri’ar Bongo suka shafe suna yi a ƙasar.
Manhaja ta rawaito a ranar Laraba sojojin ƙasar suka hamɓarar da Ali Bongo Ondimba daga karagar mulki tare da soke zaɓen da aka ce Odimba ne ya lashe.
Sun ce zaɓen da ya gudana a ƙasar cike yake da maguɗi.
A ranar Talata da daddare Hukumar Zaɓe ta ƙasa ta bada sanarwar sakamakon zaɓen inda Ali Bongo ya samu ƙuri’u kashi 64.27%, yayin da abokin hamayyarsa, Ondo Ossa ya tsira da ƙuri’u kashi 30%.