•Ba za mu amince da halayyar sojoji ba, inji Shugaban Nijeriya
*Shugabannin Kamaru da Rwanda sun sauke manyan hafsoshinsu
*Ka daure ka koma Nijar – Tinubu ya roqi Sarkin Musulmi
*Hamɓararren Shugaban Gabon ya nemi agaji
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Daga dukkan alamu hamvarar da gwamnatin Ƙasar Gabon ya ɗaga hankalin wasu shugabannin Afrika bisa la’akari da yadda suke ɗaukar matakai daban-daban wajen ganin sun daƙile afkuwar hakan a ƙasashensu, inda ake ganin lamarin a matsayin kaɗuwar hanta.
A shekaranjiya Laraba, 30 ga Agusta, 2023, ne sojoji suka hamɓarar da gwamnatin Ƙasar Gabon, makonni bayan kiki-kakar da ake yi da sojojin Ƙasar Nijar, waxanda suka kifar da gwamnatin Muhamad Bazoum ranar 26 ga Yuli, 2023.
Shugaban Nijeriya ya nemi Sarkin Musulmi ya koma Nijar:
Shugaba Bola Tinubu a ranar Alhamis ya ce duk wani zaɓin diflomasiyya zai kare da gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar kafin duk wani mataki na ƙarshe na shiga tsakani na soja.
Yayin da yake karɓar mambobin Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, shugaban ya nanata cewa duk wani yunƙuri na hamɓarar da gwamnatin dimukraɗiyya ya kasance “ba za a amince da shi ba.”
Ya ce ba a yi amfani da madadin sa baki a jamhuriyar Nijar ba.
“Dole ne in gode muku saboda ziyarar da kuka kai a Jamhuriyar Nijar, Mai martaba, amma za ku koma. Tsorona ya ƙara tabbata a Gabon.
“Mu maqwabta ne da Jamhuriyar Nijar, kuma abin da ya haɗa ’yan Nijeriya tare da manyan mutanensu ba zai iya karya ba. Babu wanda ke sha’awar yaqi. Mun ga irin varnar da aka yi a Ukraine da Sudan. Amma, idan ba mu yi amfani da babbar sanda ba, dukkanmu za mu sha wahala,” inji shi.
Shugaban ya ce Nijeriya a ƙarƙashin Janar Abdulsalami Abubakar, ta kafa shirin miƙa mulki na watanni tara a shekarar 1998, kuma ta samu nasara matuƙa, wanda ya kai ƙasar cikin wani sabon yanayi na mulkin dimukraɗiyya.
Shugaban ya ce bai ga dalilin da zai sa ba za a yi irin wannan a Nijar ba, idan har hukumomin sojin ƙasar na da gaskiya.
”Mai Alfarma, kada ka gaji don Allah, za ka sake komawa Nijar. Ba za a amince da halayyar sojojin ba.
Idan suka yi sauye-sauye cikin gaggawa, to mu ma cikin hanzari za mu sassauta takunkuman da muka ƙaƙaba musu, domin rage wahalhalun da muke gani a ƙasar,” inji shugaban na Ecowas.
Tun farko dai, shugabannin soji na Nijar da suka hamɓarar da Shugaba Bazoum Mohamed sun bayyana cewa ba za su wuce tsawon shekara uku a kan mulkin ƙasar ba.
Sai dai, ƙungiyar Ecowas ta yi watsi da wannan matsayi.
Dangane da wahalhalun da ‘yan Nijeriya da dama ke fuskanta bayan cire tallafin man fetur, shugaban ya ba da tabbacin cewa duk wani gyare-gyaren da ake yi zai ‘yantar da tattalin arzikin ƙasar, wanda zai amfanar da mafi yawan al’ummar ƙasar ta fuskar damammaki, ababen more rayuwa, kiwon lafiya da ilimi.
“Nijeriya na shirin yin alƙawari. Bambance-bambancenmu zai juya zuwa wadata, ba wahala ba. Za mu gina ƙasar da ‘ya’yanmu za su yi alfahari da ita,” inji Shugaban.
Shugaban ya shaida wa tawagar cewa, gwamnatin tarayya ta buɗe tattaunawa da gwamnatocin jihohi domin samar da filayen da za a riƙa ciyar da dabbobi yadda ya kamata da nufin bunƙasa kiwon dabbobi na ƙasa baki ɗaya da kuma hada-hadar noma da sarrafa kayayyakin amfanin gona na fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje da samar da ayyukan yi da kuɗaɗen shiga.
“Idan har yanzu Nijeriya na neman alluran rigakafin al’amuran lafiya; idan mace-macen jarirai da mata masu juna biyu ya zama ruwan dare, to mu bincika kanmu. Zan yi alƙawarin tuntuvar wasu shugabanni, kamar NSCIA, kuma za mu biya buƙatun jama’armu,” inji shi.
Da yake jawabi a wajen taron, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce shugaban ƙasar ya ware Naira biliyan 50 domin tallafa wa ayyukan sake gina rayuka da dukiyoyi a yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, tare da mayar da hankali kan tattaunawa don magance matsalolin tsaro.
Sarkin Musulmi ya yi alƙawarin yin biyayya ga Shugaban Ƙasa ɗari bisa ɗari, yana mai tabbatar da cewa shugaban zai kai ga ci da yardar Allah.
A nasa jawabin, Mai Martaba Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya tabbatar wa shugaban ƙasar cewa hukumar NSCIA za ta kasance a shirye don bayar da shawarwari da goyon bayan gwamnati mai ci, inda ya ƙara da cewa “Allah zai yi wa dukkan shugabanni hisabi, bisa adalci da gaskiya.
Ya ce kamata a sanya ido a kuma qara ƙaimi wajen rabon kayayyakin jinƙai a faɗin ƙasar nan, don kaiwa ga mutanen da ke cikin mawuyacin hali.
Shugabannin Kamaru da Rwanda sun kori manyan hafsoshin soji juyin mulkin Gabon:
Shugaban ƙasar Rwanda Paul Kagame da takwaransa na Kamaru Paul Biya ɗan shekaru 90 a duniya sun kori hafsoshin sojinsu sa’o’i 24 bayan da sojoji suka karɓi ragamar mulkin ƙasar Gabon.
A birnin Kigali, Kagame ya kori hafsoshin soji kusan 200, da suka haɗa da janar-janar guda huɗu, James Kabarebe da Fred Ibingira, da janar-janar guda uku Charles Kayonga da Frank Mushyo Kamanzi, kamar yadda jaridar New Times ta ƙasar Rwanda ta ruwaito a ranar Larabar da ta gabata, ta naƙalto wata sanarwar gwamnati.
Shugaban na Rwanda, wanda ya yi fice wajen murƙushe kafafen yaɗa labarai da ‘yan adawa, ya kuma yi wa manyan hafsoshi 83 ritaya, ƙananan jami’ai 06 da manyan hafsoshi 86 da ba na gwamnati ba, yayin da 160 aka sallame su saboda rashin lafiya” sanarwar ta ce.
A Kamaru, Mista Biya, wanda ke shafe mafi yawan lokutansa a Switzerland, shi ma nan take ya sallami jami’an soji da na sama da na ruwa.
Sauye-sauyen da aka samu a ƙasashen Kamaru da Ruwanda ya zo ne kwana guda bayan juyin mulkin da aka yi a Gabon, inda aka hamɓarar da Shugaba Ali Bongo Ondimba tare da tsare shi da sojoji suka yi.
Shugabannin biyu dai ba su yi tsokaci kan juyin mulkin da aka yi a Nijar da Gabon ba a cikin hukuncin da suka yanke.
Sojojin da suka ƙwace mulki a Nijar a ƙarshen watan Yulin da ya gabata, sun kuma fuskanci takunkumi daga Ƙungiyar ECOWAS, ko da yake kawo yanzu matakan sun kasa shawo kan gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta mayar da mulki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.
Biya, a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Tuwita da yammacin Laraba, ya ce ya bayar da sanarwar korar wasu sojoji tare da kwashe wasu daga ma’aikatar tsaron ƙasar.
Sabbin manyan hafsoshin soji da aka naɗa a rundunar sun haxa da Ajeagah Njei Felix, Kamdom Lucas, da Nguema Ondo Bertin Bourger, da dai sauransu.
Edou Essono Serge Durel da Moudio Hervé na daga cikin sabbin jami’an da aka naɗa a cikin tekun Kamaru.
Biya ya karɓi mulki ne a shekarar 1982 yana da shekaru 49. Ya jagoranci al’ummar ƙasar tun daga lokacin. Kafin ya zama shugaban qasa, ya tava zama firaminista daga shekarar 1975 zuwa 1982.
Tsawon shekaru da dama da gwamnatinsa ta yi, ba ta da wani babban tasiri ga tattalin arzikin ƙasar Kamaru, inji masu suka.
Shugaba Bongo ya roƙi ƙasashen duniya su kai masa ɗauki:
Shugaban Gabon, Ali Bongo, wanda ke cikin yanayi na ɗaurin talala bayan juyin mulkin da sojoji suka yi masa, ya nemi ƙasashen duniya da abokansa su kai masa ɗauƙi.
A wani bidiyo da aka fitar a shafukan sada zumunta an ga Mista Bongo a inda ya ke tsare yana magana da harshen Turanci yana cewa, shi da iyalinsa na tsare, sai dai kuma bai san halin da matarsa da ɗansa ke ciki ba.
“Ina aika saƙo ne kawai ga duk abokan da muke da su a duk duniya. Don yin magana. Mutanen nan sun kama ni da iyalina,” Mista Bongo ya shelanta.
Ya koka da yadda masu juyin mulkin suka hana shi ganawa da matarsa da ɗansa, suna masu cewa, “Ban san abin da ke faruwa ba”.
“Ina kiran ku don kawo min ɗauki, ku yi kwarmato,” inji shi.
Masu juyin mulkin da suka bayyana a gidan talabijin na Gabon sun kuma yi watsi da nasarar Mr Bongo a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Sojoji da suka kifar da gwamnatin Bongo sun rushe gwamnatinsa tare da rufe iyakokin ƙasar, su na masu jadadda cewa jagoran juyin mulkin ne zai riƙe ƙasar.
Zuri’ar iyalan Bongo sun shafe shekaru 56 akan mulkin Gabon.