Juyin mulkin Nijar: Bazoum ya sha alwashin gwagwarmayar kare dimukraɗiyya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Muhammad Bazoum, Shugaban Ƙasar Nijar, wanda sojoji suka yi wa juyin mulki a ranar Laraba, ya ce, ya sha alwashin kare ribar dimokraɗiyya da suka sha yin gwagwarmaya a kai wajen nema wa al’ummar ƙasar ‘yanci.

Rahotanni sun ce, Mohamed Bazoum na tsare a hannun waɗanda suka shirya maƙarƙashiyar yi masa juyin mulki, waɗanda tun farko suka sanar da dakatar da duk wasu cibiyoyin gwamnati a ƙasar.

Ita ma rundunar sojojin Nijar ta yi watsi da juyin mulkin da aka yi wa shugaban ƙasar. Babban hafsan sojin qasar ya ce, yana buƙatar “kiyaye mutuncin taɓa lafiyar” shugaban ƙasa da danginsa tare da kauce wa “mummunan rikici, wanda zai iya haifar da zubar da jini da kuma shafar tsaron jama’a”.

A yayin da rahotanni ke nuni da cewa, masu yunƙurin juyin mulkin na hannun daman Bazoum, waɗanda tun da farko suka sanar da dakatar da hukumomin gwamnati da kuma rufe iyakokin Nijar, Bazoum ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa: “za mu ci gaba da gwagwarmaya don kiyaye nasarorin da aka samu da kuma dukkan ‘yan Nijar masu ƙaunar dimukraɗiyya..”

Ministan harkokin wajen ƙasar, Hassoumi Massoudou, ya yi wani kira a shafinsa na Tuwita na “dukkan ‘yan dimukraɗiyya da masu kishin ƙasa” kada su amince da juyin mulkin. Massoudou ya ce, “ikon da ya dace da doka” shi ne wanda zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya yi amfani da shi, yana mai jaddada cewa duk da cewa an yi yunƙurin juyin mulki, dukkan sojojin ƙasar ba su da hannu.”

“Muna roƙon duk sojojin da ke da rauni su koma ga aikinsu,” inji shi. 

“Za a iya cimma komai ta hanyar tattaunawa amma dole ne hukumomin jamhuriyar su yi aiki.”

“Nijar babbar ƙawa ce ga Faransa da Amurka a yaƙin da ake yi da ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.

“Matsayin ƙasar ya ƙaru ne tun bayan da dangantaka da Burkina Faso da gwamnatocin sojojin Mali suka yi tsami, lamarin da ya janyo janyewar sojojin qasashen waje.”

A cikin watan Mayu, Bazoum ya koka da cewa, gwamnatinsa ta kasance maƙasudin yaqin neman zave daga ƙungiyar Wagner ta Rasha, wacce ta kasance ta yi tasiri wajen dagula zaman lafiya a wasu wurare a yankin.

Ba a dai san ko nawa ne masu yunƙurin juyin mulkin suka mamaye Nijar ba. A wani jawabi da suka yi a gidan talabijin na qasar a ranar Laraba, sojoji sun sanar da cewa an cire Bazoum daga kan karagar mulki, kuma an dakatar da dukkan hukumomin jamhuriyar, a juyin mulki karo na bakwai da aka yi a Yammaci da Tsakiyar Afirka tun daga shekarar 2020.

Matakin na tumɓuke Bazoum, ƙasashen duniya sun yi Allah wadai, ciki har da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, wanda ya ce ya yi magana da Bazoum.

“Na miƙa goyon bayanmu ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Nijar bisa tafarkin dimokuraɗiyya. Amurka ta yi Allah-wadai da qoqarin murguɗa tsarin mulkin Nijar da qarfi, kuma ya jaddada cewa ƙawancenmu ya dogara ne kan ci gaba da gudanar da mulkin dimokuraɗiyya,” inji Blinken a shafin Tuwita.

Ƙungiyar Tarayyar Afirka da Ƙungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka sun yi tir da juyin mulkin, yayin da babban sakataren MDD, António Guterres, ya buqaci a mutunta kundin tsarin mulkin Nijar.

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce takwaransa na qasar Benin, Patrice Talon, na tafiya Nijar ne domin shiga tsakani. “Yanzu yana kan hanyarsa,” inji Tinubu, wanda shi ne Shugaban ECOWAS, bayan ganawarsa da Talon a Abuja.

A safiyar ranar Alhamis ne aka bayar da rahoton cewa, babban birnin ƙasar Yamai, ya yi tsit, yayin da aka bayyana rufe iyakokin ƙasar da kuma filayen jiragen sama. Tare da saka dokar fita.

Magoya bayan Bazoum da dama ne suka taru a birnin a daidai lokacin da al’amura ke gudana a ranar Laraba, inda suke bayyana adawarsu da sauya madafun iko, inji wani ɗan jarida na Reuters. Inda daga baya ya ce aka tarwatsa su.

Jami’an tsaron Fadar Shugaban Ƙasar da suka fara kai hari kan Bazoum, na ƙarƙashin jagorancin Janar Omar Tchiani ne, amma wani jami’in sojin sama, Kanar Amadou Abdramane ne ya karanta sanarwar ta gidan talabijin.

Abdramane wanda shi ne ya karanta sanarwar a gidan talabijin na ƙasar, ya ce jami’an tsaro sun dauki matakin ne sakamakon taɓarɓarewar tsaro da rashin shugabanci na gari da Bazoum ke gudanarwa.

Ƙasar Nijar da ba ta yawan jama’a, tana ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci da rashin kwanciyar hankali a duniya.

Ta yi juyin mulki huɗu tun bayan samun ‘yancin kai daga Faransa a 1960, da kuma yunquri da dama, ciki har da biyu a baya kan Bazoum.

Bazoum, mai shekaru 63, na ɗaya daga cikin gungun shugabannin ƙasashen Yammacin Duniya da ya rage a yankin Sahel, inda rikicin ‘yan jihadi ya haifar da juyin mulki akan zaɓaɓɓun shugabannin ƙasashen Mali da Burkina Faso.

Dakarun mulkinsu, sun ɗauki matakin kishin ƙasa, sun kori sojojin Faransa, kuma a ɓangaren Mali sun qulla ƙawance da Rasha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *