Juyin wainar siyasar Zamfara: Dattijon ƙasa, Hassan Nasiha, ya koma na’ibin Matawalle

*Shin gaba Sanata Nasiha ya ci ko kuwa baya?

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Daga dukkan alamu siyasar Jihar Zamfara na cigaba da zama wahainiyar da ke rikiɗa tana yin juyin wainar da ba a saba gani ba a tarihin siyasar Nijeriya bakiɗaya. Idan za a iya tunawa, a shekara ta 2019 kwana ɗaya kafin rantsar da sabuwar gwamnati ne bakiɗayan waɗanda aka zaɓa a tutar ƙarƙashin Jam’iyyar APC a jihar, Kotun Ƙolin Nijeriya ta kore su a yayin da ta yanke hukuncin da ya ɗora ilahirin ’yan takarar Jam’iyyar PDP, waɗanda bakiɗayansu sun faɗi zaɓe a lokacin da aka kaɗa ƙuri’a. Don haka sai ya zamana a mataki na jiha ko tarayya babu ’yan APC ko guda, waɗanda aka rantsar. Hujjar Kotun Ƙoli ita ce, ba a cika ƙa’ida wajen tsayar da su takara ba.

To, a shekaranjiya ne kuma aka sake yin wani juyin wainar, inda mai riƙe da muƙamin sanata, wato dattijan ƙasa a Majalisar Dattawa sukutum, ya koma Mataimakin Gwamna; ba fa gwamna ba! Abin nufi a nan shine, daga aikin dattijantaka na bai wa hatta Shugaban Ƙasa umarni, yanzu ya koma ɗan aike ko na’ibin gwamnan jihar, Muhammad Bello Matawalle, wanda har kawo yanzu ba a gwada shi da quri’a, ya lashe zaɓe ba. Bari mu fara sanin wane ne wannan sanata da ya koma Mataimakin Gwamna?

Hassan Muhammadu ‘Nasiha’ shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Muhalli da ɗumamar Yanayi har zuwa ranar Laraba 23 ga Fabarairu, 2022, a lokacin da aka rantsar da shi a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara bayan da rikita-rikitar siyasar jihar ta kai ga tsige Mahdi Aliyu Gusau daga kujerar.

Alhaji Hassan Muhammad Nasiha kwatsam Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta neme shi ne da ya miƙa takardunsa, inda ya dauki jakarshi ya tafi gaban majalisar, wacce nan take ta tabbatar da shi a cikin mintuna biyar.

A Jihar Zamfara, Sanata Hassan Nasiha, suna ne da ke kaɗa ƙararrawa, domin kowa ya san shi mutum ne da ke iya sadaukar da kansa a harkar siyasar jihar a koyaushe. Kafin Gwamna Ahmed Yarima ya naɗa shi kwamishina a 1999, Sanata Nasiha ya samu nasarar gudanar da rukunin kantin magani a jihar mai suna Nasiha Pharmacy, ya kuma fara sana’ar ruwan leda na farko a jihar mai suna Nasiha Table Water. Wannan ya gwada cewa, Sanata Nasiha ba ƙaramin mutum ba ne a jihar ta Zamfara, amma bari mu ji tarihin rayuwarsa.

Taƙaitaccen tarihinsa:
An haifi Hassan Muhammadu Nasiha a ranar 12 ga Disamba, 1960, a Gusau, wanda ya zamo ƙwararren ma’aikacin jinya, bayan da ya samu takardar shaidar kammala aikin jinya da ungozoma daga makarantar koyon aikin jinya da ke Sakkwato.

Ya samu sunan Nasiha ne a harkar kasuwancinsa, amma kafin ya shiga harkar kasuwanci ya yi aikin jinya a gefen gado a babban asibitin garin Gusau na tsawon shekaru. Bayan haka, ya fara sana’ar sayar da magunguna. Haka zalika, a lokacin da ake tunkarar zaɓukan 1999, an ce Hassan Nasiha ya goyi bayan ɗan takarar jam’iyyar ‘All People’s Party’ (APP) na lokacin, Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura, da gagarumar gudummawar kuɗi.

Ya kuma bai wa masu biyayya ga jam’iyyar magunguna kyauta a lokacin da aka zaɓi Yarima. Nasiha na cikin waɗanda aka naɗa a matsayin kwamishina.

Da farko, an tura shi Ma’aikatar Lafiya, sannan kuma Ma’aikatar Kasuwanci da Masana’antu. Ya kuma kasance Kwamishinan Muhalli, Albarkatun Ruwa, Filaye da Gidaje da kuma Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu daga 1999 zuwa 2003.

Siyasarsa a 2007:
A yayin da ake tunkarar zaɓukan 2007, Hassan Nasiha da wasu ’yan siyasa daga shiyyar Sanatan Zamfara ta Tsakiya, musamman Gusau, Babban Birnin Jihar, sun fara yaƙin neman zaɓen kujerar Gwamnan Jihar, don tabbatar da ɗan takararsu ya fito a Gusau.

Haka zalika Kakakin Majalisar Dokoki, Mamman Bawa; Bature Umar (Kwamishina) Sambo, Ɗanbuba Gusau (Kwamishina) da dai sauransu sun ƙudiri aniyar sanya Yarima ya zaɓi gwamna a cikinsu, kamar yadda ƙaddara ta tabbata, tsohon gwamna, Mahmud Shinkafi, ya fito.

Nasiha, wanda a lokacin ya zama mai tasiri, an ba shi tikitin wakiltar yankin Majalisar Dattawa. A Majalisar Dattijai, an naɗa shi a kwamitocin Kimiyya da Fasaha, Asusun Jama’a, Sufurin Ruwa, Lafiya, Gas da Ayyuka. 

Amma ya yi shekara huɗu kacal (2007– 2011) lokacin rikicin ‘Yarima – Yari Tsunamin na Siyasa’ ya shafe su, sai ya fice daga ANPP zuwa PDP. Kabiru Marafa na jam’iyyar ANPP ne ya doke shi Hassan Nasiha a shekarar 2011.

Shekaru takwas da Abdulaziz Yari ya yi yana mulkin Jihar Zamfara, Hassan Nasiha, ya ci gaba da zama a jam’iyyar adawa ta PDP kuma ya kasance shugabanta daga 2015 zuwa 2019 lokacin da ya sake lashe kujerar Sanata a ƙarƙashin jam’iyyar PDP ta hannun Kotun Ƙoli.

Haka zalika wasu masana harkokin siyasa da dama na iya ganin cewa, wani sanata kuma Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai Kula da Muhalli da Sauyin Yanayi, ya bar muƙaminsa ya amince ya zama mataimakin gwamna, kamar wani ci-baya ne a gare shi.

Wasu kuma na iya cewa, da irin tasirin da ya ke da shi a kan Gwamna Matawalle, sabon Mataimakin Gwamnan ba zai samu matsala ba wajen cigaba da riƙe kujerarsa ta Majalisar Dattawa a lokacin wani zaɓen. 

To, me ya sa a ce za a zama mataimakin gwamna, aikin da aka saba yi wa izgili a Nijeriya a matsayin na ‘yar taya murna? Sanata Nasiha dai ya sa ido a kan kujerar gwamnan jihar tun a shekarar 2007. Haka kuma wasu masana harkar siyasar Nijeriya sun yi imanin cewa, matakin da ya ɗauka na fafutukar neman kujerar, wani ƙoƙari ne na ganin ya samu kansa a fagen siyasar jihar, domin cika burinsa na zama gwamna a 2027. Ya aka yi lamarin ya faru?

Yadda Hassan Nasiha ya sadaukar da kujerarsa ta sanata:
’Yan sa’o’i kaɗan bayan samun rahoton kwamitin binciken zarge-zarge akan mataimakin gwamnan jihar Zamfara Mahdi Aliyu Gusau, Majalisar Dokokin Jihar ta tsige shi a ranar Laraba, an kuma rantsar da wani ɗan majalisa mai ci, Sanata Hassan Mohammed Nasiha, a matsayin wanda ya maye gurbinsa.

Mataimakin gwamnan da aka tsige ɗan Janar Mohammed Gusau (mai ritaya) ne, wani ƙwaƙƙwaren soja kuma hamshaƙin ɗan Nijeriya wanda aka fi sani da Mista Spy, haka nan ɗaya daga cikin dattawan ƙasa.

Kwamitin binciken Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ya miƙa rahoton ga majalisar, sannan Kakakin Majalisar, Rt. Hon Nasiru Mu’azu Magarya, ya karanta a zauren majalisar. Magarya ya shaida wa zauren taron cewa, kwamitin da aka kafa, domin binciken tsohon mataimakin gwamnan ya same shi da laifukan da ake tuhumar sa da shi, kuma ya umarci takwarorinsa da su cigaba da kaɗa ƙuri’ar amincewa da tsige mataimakin, kamar yadda doka ta tanada nan take. Daga nan ne magatakardan majalisar, Shehu Saidu Anka, ya kafa kwamitin kaɗa ƙuri’a, inda ake kiran kowane ɗan majalisa bisa jerin sunayen mazaɓarsa.

A ƙarshen ƙuri’ar, mambobi 20 cikin ashirin 22 ne suka kaxa ƙuri’ar amincewa da tsige shi, yayin da ɗan majalisa daga Jam’iyyar PDP, Salihu Usman Zurmi, bai fito fili ba a zaman majalisar na ranar Laraba da ya gabata.

Bayan samun adadin ƙuri’un da ake buƙata, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, Kakakin Majalisa Magarya ya sanar da tsige tsohon mataimakin Gwamnan Mahdi Aliyu Gusau daga muƙaminsa. Daga nan sai ya gabatar da sunan wanda Gwamnan Jihar, Bello Matawalle, ya miqa wa majalisar, don amincewa da shi a matsayin sabon mataimakonsa.
“Ta hanyar sashe doka na 1999, mambobin sun tabbatar da zaɓen Sanata Hassan Mohammed Gusau a matsayin sabon Mataimakin Gwamna,” inji kakakin.

Bayan haka, ‘yan majalisar sun tantance Nasiha tare da tabbatar da shi a matsayin mataimakin Gwamna Bello Mohammed Matawalle nan take.
Da ya ke ƙaddamar da sabon mataimakin gwamnan, Gwamna Bello Mohammed Matawalle, ya buƙace shi da ya mara wa gwamnatinsa baya wajen cigaban jihar.

Matawalle, wanda ya bayar da tabbacin samun kyakkyawar alaƙa da mataimakin gwamnan, ya kuma buƙaci tsohon ɗan majalisar da ya fito da wasu tsare-tsare, don magance matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar.

Ya ce zaɓin Nasiha ya samo asali ne sakamakon tuntuɓar juna da aka yi da kuma yadda ya jajirce wajen ci gaban jihar a Majalisar Dattawan ƙasar.

Gwamna Matawalle ya yaba wa ‘yan majalisar jihar bisa jajircewar da suka yi da kuma yadda suka bi kundin tsarin mulki wajen tsige tsohon mataimakinsa.

A jawabinsa na godiya, sabon Mataimakin Gwamnan, Sanata Hassan Nasiha, ya yi alƙawarin yin aiki tare da ofishin gwamnan domin haɗin kai da ci gaban jihar.

Gusau ya fara fuskantar matsin lamba ne bayan ƙin sauya sheƙa daga PDP zuwa APC, kamar yadda Gwamna Matawalle ya yi a shekarar da ta gabata, inda ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Mutanen biyu sun hau kujerar jagorancin jihar ne a ƙarƙashin jam’iyyar PDP bayan hukuncin Kotun Ƙoli da ta haramta ’yan takarar jam’iyyar APC a zavien 2019 tun farko.
Haka zalika, majalisar ta miƙa wa mataimakin gwamnan sanarwar tsige shi ta hannun sakataren gwamnatin jihar kafin ta buƙaci Babban Alƙalin Alƙalan Jihar ya kafa kwamitin bincike domin tabbatar da zargin da ake masa.

Majalisar ta bakin shugaban yaɗa labarai na majalisar, Hon. Shamsudeen Basko, ya ce ana zargin mataimakin gwamnan da laifuka uku.
Laifukan kuwa su ne, “cin zarafin ofishinsa, cin zarafin kai ta hanyar yin amfani da kuɗin jama’a da kuma rashin sauke nauyin ayyukan hukuma.”

Hon.  Basko ya ce: “Zargin ofis. Wannan ya haɗa da saɓa wa sashe na 190 da na 193 (1), (2) (a) (b) (c), na kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya 1999 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima).

“Yunƙurin wadatar da kai da laifuka ta hanyar amfani da kuɗaɗen gwamnati; ya haɗa da karkatar da kuɗaɗen jihar da laifin damfarar gwamnati, da haɗa baki da zamba a jihar da kuma ƙin amincewa da yin murabus a ofishin sa. Rashin sauke ayyukan tsarin mulki, wanda ke haifar da rashin biyayya,” inji shi.

Yanzu an zura ido yadda za ta kaya da sabon Mataimakin Gwamnan, la’alla gaba ya ci ko baya!