Ka ƙyale Matawalle ka fuskanci aikin da ke gabanka, kiran ƙungiya ga Gwamnan Zamfara

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Progressives Congress (APC) Defense Coalition na babban zaɓen 2023 ta yi kira ga Gwamnan Jihar Zamfara, Lawal Dauda da ya maida hankali wajen yi wa jihar aiki maimakon ɓata lokaci wajen faɗa da tsohon Gwamnan jihar, Bello Matawalle.

Ƙungiyar ta ce Bello ya bar Naira biliyan 2.5 a asusun jihar, kuma ya taɓuka wajen tattalin kadarorin jihar da ma fannin tsaro don amfanin jihar baki ɗaya.

Ta ƙara da cewa, iƙirarin da Dauda ya yi kan cewa tsohon Gwamnan bai bar komai a asusun jihar ba, hakan wani yunƙuri ne na hana a yi wa tsohon gwamnan yabon da ya cancanta.

Yayin da suke yi wa manema labarai jawabi ranar Asabar a Abuja, Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dr Shuaibu Suleiman Shinkafi da Sakataren ƙungiyar, Comrade Anas Abdullahi Kaura, sun ce iƙirarin da Gwamna Dauda ya yi ba sahihi ba ne.

Ƙungiyar ta ce Gwamna Bello Matawalle ya yi bakin ƙoƙarinsa wajen tabbatar da talakawan Zamfara ya samu walwala.

Ta ƙara da cewa, a halin yanzu al’ummar jihar ba su da wani buri da hanƙoro face ganin yadda gwamnati mai ci za ta yi amfani da abin da jihar ke da shi a ƙasa wajen ci gaba da kyautata rayuwar talakawan jihar.