Ɗangote na siyan mota biyu kacal a shekara takwas – Davido
Daga AISHA ASAS
Shahararren mawaƙi David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, a cikin wata tattaunawar da ya yi da Forbes, ya bayyana kyakyawar alaƙa da ke tsakanin sa da babban ɗan kasuwa, Aliko Ɗangote.
A cikin tattaunawar, Davido ya yi muhimman batutuwa da suka haɗa da irin shawarar da Ɗangote ya fi yawan ba shi a duk lokacin da suka haɗu.
Shawarar da za mu iya cewa, da yawa mutane sun yi mamakin fitowarta daga babban mai kuɗi irin Ɗangote.
Da yawa idan ka tarar da wani yana ‘lissafin duna’, kan lamarin samun dukiya, za ka tarar yana lissafa yadda zai ci mutuncin kuɗi, ta hanyar siyan ababen da zuciya ta yi muradi, idan har aka waye gare ya zama mai arziki.
Kamar yadda masu azancin magana suka ce, wai kuɗi da maciji, maganinsu kashi, don haka a yayin da ake kallon wanda ya fi kowa arziki a Afrika, zukata da dama kan tafi kan ƙiyasta irin facaka da tariyyar ababen more rayuwa da yake yi.
Wannan ce ta sa, zai zama abin mamaki idan ya kasance irin wannan mutum mai tarin arziki na yi wa wani nasiha kan ya yi tattalin kuɗaɗen shi.
Mawaɗi Davido ya bayyana cewa, a duk lokacin da suka haxu da Ɗangote, wanda ya kasance amini ga maihaifinshi, wato Chief Adedeji Adeleke, yana yawan ba shi shawara kan tattalin dukiyarshi, da kuma guje wa yawan saye-saye marasa amfani.
“A duk lokacin da muka haɗu da Kawu Ɗangote, abu ɗaya yake faɗa min, Davido, ka adana kuɗinka, babu wata shawara da ya fi ba ni kamar wannan,” inji shi.
Ya kuma ƙara da cewa, “Kawu Aliko na da bambanci sosai da sauran shahararrun masu kuɗi, domin motoci biyu kacal yake siya a cikin shekara takwas. Matuqa yana da tarbiyyar kuɗi, kuma bambancin shi da sauran masu arziki mai yawa ne.”
Mawaƙin ya ƙara da bayyana irin rawar da mai arzikin ya taka a cigaban al’ummar ƙasar nan ta hanyar samar da kamfanonin da suka wanzar da ayyukan yi ga mutanen Nijeriya.
Wannan bai kasance karo na farko da mawaƙin ya yi magana kan alaƙa da kuma yadda attajiri Ɗangote yake gudanar da rayuwarshi cikin sauƙi.
Ko a shekarar da ta gabata, mawaƙin ya bayyana a wata tattaunawa cewa, shekaru 10 kenan rabon Ɗangote da siyan sabuwar mota.
Daga ƙarshe, ya ƙarfafa alaƙarsu da Ɗangote, don ƙara tabbatar da gaskiyar maganar tasa, da cewa, Ɗangote ne ma ya ɗauko mahaifiyarsa daga asibiti a lokacin da aka haife shi.