Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar mayaƙan Nija-Delta sun yi barazanar ƙone tashoshin man da ke yankin matuƙar Shugaba Bola Tinubu ya gaza ɗaukar mataki akan Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Mayaƙan sun yi gargaɗin ne kan zargin Wike da yunƙurin ƙasƙanta gwamnatin Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas.
Kakakin ƙungiyar, Justin Alabraba ya bayyana hakan cikin wata takarda da ya fitar wa manema labarai a inda ƙungiyar ta nuna fushinta kan zargin Wike da shirya maƙarƙashiya wajen yin amfani da kusancinsa ga allƙalin da zai yin hukunci kan ƙararsu da Fubara game da kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar a ranar Litinin.
Alabraba ya ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaiɗaita tashoshin mai matuƙar aka yi hukuncin da ya goyi bayan Wike, wanda su na ganin hakan ka iya dakatar da jagororin ƙananan hukumomin cika alƙawarin da suka yi wa al’ummominsu.
Ya ƙara da cewa, matuƙar Tinubu ya ƙyale Wike ya hargitsa shugabancin ƙananan hukumomi a Ribas, to za su hargitsa shugabanci a kowane mataki, ya na mai cewa ba za su cigaba da shan wahala ba yayin da wasu ɓangarorin Nijeriya ke ci-gaba, don haka Wike ya sake wa Fubara mara.