Daga BELLO A. BABAJI
Fadar shugaban ƙasa ta yi tsokaci game da kalaman Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed na cewa Shugaba Bola Tinubu bai sauron koken al’umma, inda ta yi kira a gare shi da ya mayar hankali akan jagorancin jiharsa.
A farkon makon nan ne gwamnan ya gana da jigon ƙungiyar Izala na ƙasa reshen Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir game da halin da ƙasar take ciki.
Sheikh Jingir ɗaya ne daga cikin jagororin da suka tallata tikitin Muslim-Muslim wanda hakan ya kai ga samun nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen 2023.
Gwamnan ya ce lallai ne babu jituwa tsakaninsu da shugaban ƙasa ganin yadda al’umma suke halin matsi a ƙasar, amma duk da haka, ko su gwamnoni bai sauraron su.
Ya ce yankin da tsare-tsaren Tinubu ya fi shafa shi ne Arewa, ya na mai cewa sauya fasalin haraji da Gwamnatin Tarayya take ƙoƙarin yi zai ƙara ta’azzara taɓarɓarewar yankin.
Saidai, mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare ya ce siyasa ce mara amfani gwamnan ke yi.
Ya ce kamata yayi a ce gwamnan ya mayar da hankali kan jagorancinsa na jiha, ba amfani da Shugaba Tinubu wajen rufe laifinsa ba.
Ya kuma ce Shugaba Tinubu ya duƙufa ne wajen farfaɗo da tattalin arziƙin Nijeriya wanda zai yi hakan ne a tsawon shekaru huɗu.
Ya ƙara da cewa, Gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali ne wajen samar da ayyukan ci-gaba da yadda za a inganta zamantakewar ƴan Nijeriya.
Har’ilayau, game da sauya fasalin haraji, Dare ya ce duk ɓangaren da ya ga akwai matsala game da zartar da shi, zai iya bin hanyoyin da doka ta tsara wajen bayyana ra’ayinsa tun da abu da aka gina shi a hukumance.