Kada a jefa rayuwar Shettima cikin haɗari, yana buƙatar sabon jirgi – Kakakin Majalisar Borno

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Rt. Hon. Abdulkarim Lawan, ya bayyana damuwa kan rayuwar Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, yana cikin haɗari saboda matsaloli da jirgin mataimakin shugaban ƙasan ke fuskanta. Lawan ya yi wannan magana ne bayan da Shettima ya soke tafiyarsa zuwa taron Ƙolin Commonwealth a Samoa, sakamakon wani abu da ya bugi jirgin nasa a filin jirgin JFK a birnin New York, Amurka.

Lawan ya bayyana cewa jirgin da ake amfani da shi wajen wakiltar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na fama da matsaloli, kuma hakan na iya jefa rayuwar Mataimakin Shugaban Ƙasa cikin haɗari. Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar wa Shettima sabon jirgin sama domin guje wa faruwar wani lamari makamancin haka.

Bayo Onanuga, mai ba da shawara na musamman ga shugaban ƙasa, ya bayyana cewa wasu sassa na jirgin, ciki har da gilashin wajen matuƙin jirgin sun lalace sakamakon wannan haɗari. Wannan matsala ta sa Shettima ba zai iya halartar taron a Samoa ba.

Lawan ya ce, “Ina miƙa godiyata ga Allah don ceton rayuwar Shettima da tawagarsa, tare da kira ga gwamnatin Nijeriya da ta buƙaci cikakken bincike daga gwamnatin Amurka game da lamarin. Ya jaddada cewa tsohon jirgin yana da matsaloli kuma yana buƙatar a sauya shi.

Tun da farko, kwamitin majalisar wakilai kan tsaro da bincike ya yi kira ga gwamnati da ta samo sababbin jirage ga Tinubu da Shettima, sai dai amincewa da sabunta jirgi ya kasance ga Tinubu ne kawai bayan fadar shugaban ƙasa ta fuskanci tsangwama daga jama’a.