Kaduna: Ana ci gaba da binciken gano sarakunan da suka ɓace

Daga FATUHU MUSTAPHA

A halin da ake ciki, jami’an tsaro a jihar Kaduna sun bazama bincike domin gano wasu masu rawani su uku da suka ɓata a masarautar Atyap cikin ƙaramar hukumar Zangon Kataf waɗanda aka sace su bayan kammala wani taron sulhu da suka gudanar a Lahadin da ta gabata.

A cewar Gwamnatin Jihar Kaduna, mutum shida ne suka ɓata da farko a kan hanyarsu ta komawa gida bayan taron. Ta ce jami’an tsaro sun samu nasarar gano mutum guda daga cikinsu kuma sun miƙa shi ga ‘yan sanda, kana wasu mutum biyu daga ciki sun tsere daga hannun ‘yan fashin, yayin da har yanzu ba a san inda ragowar mutum ukun suke ba, in ji Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan.

Aruwan ya ce, “Jagororin sun ɓata ne bayan wani taron sulhu da aka gudanar a Lahadi, inda aka biya diyya ga waɗanda shanu suka yi wa ɓarna a gona ƙarƙashin kulawar makiyaya, kamar yadda jami’an tsaro suka kai wa gwamnatin Kaduna rahoto.

“Bayanan da aka tattara sun nuna Sakataren Dakacin Gundumar Gora, Ayuba Bungon tare da wasu, na daga cikin waɗanda aka yi taron da su lami lafiya, amma sun ɓace a hanyarsu ta komawa a motarsa. Sai dai daga bisani an gano motar a farfashe babu kowa a cikinta.

“Sakamakon matse bincike da jami’an tsaro suka yi a wannan dare sun gano Sakataren tare da miƙa shi ga ‘yan sanda.

“Daga baya, an sake gano wasu mutum biyu da suka tsere a hannun ‘yan, wato, Yusuf Dauda da Gomna Audu. Sojoji sun bada tabbacin duka su biyin lafiyarsu ƙalau kuma an miƙa wa ‘yan sanda su.

“Har yanzu saura mutum uku waɗanda ba a kai ga gano su ba. Su ne: Arɗo Pate Usman Kurmi (Wakilin Fulanin Masarautar Atyap), Arɗo Muhammadu Anchau da kuma Yakubu Muhammadu.

“Gwamna Nasir El-Rufai ya yaba da ƙoƙarin jami’an tsaron tare da buƙatar su zage damtse. Kazalika, ya yi kira ga al’ummar Masarautar Atyap da ma iyalan waɗanda lamarin ya shafa, da su kwantar da hankulansu yayin da jam’ian tsaro za su ci gaba da zurfafa bincike domin kuɓutar da su.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *