Kaduna: ‘Ba mu wakilta kowa don sasantawa da ‘yan fashi ba’ – Aruwan

El-Rufai

Daga FATUHU MUSTAPHA

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sha alwashin hukunta duk wanda ta kama yana sasantawa da ‘yan fashi ko ‘yan ta’adda a jihar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Lahadin da ta gabata.

Kwamishinan ya ce Gwamnatin Kaduna ba ta wakilta kowa ba don shiga tsakaninta da ‘yan fashi, tare da ƙaryata rahoton da ke cewa Gwamnatin Nasir El-Rufai ta naɗa wasu wakilai domin tattaunawa da masu aikata muggan laifuka a jihar.

Sanarwar Kwamishinan ta buƙaci ‘yan jihar da su kai rahoton duk wanda ya doge a matsayin jami’in gwamnati wajen tattaunawa da ‘yan ta’adda don ya fuskanci fushin gwamnati.

Jihar Kaduna na daga cikin sassan da ke fama da ‘yan fashi masu satar mutane, wanda ko a kwanakin baya sai da ɓatagarin suka kai wa Sarkin Birnin Gwari hari amma ba su same shi ba.