Kafar sadarwa na taimakon mata matuƙa ta fuskar kasuwanci – Maryam Ango

Da wuya kaga an wulaqanta macen da ke da ilimi da aiki da shi”

Daga AISHA ASAS

A yau shafin Gimbiya na jaridarku mai farin jini, Manhaja, ya zaƙulo maku ɗaya daga cikin mata matasan da suka canza kallon da ake yi wa mata ta ɓangaren sana’a, yayin da suka yi zurfin tunani wurin amfani da zamani wurin neman na kai.

Sanannen abu ne kafafen sada zumunta sun zama wata taba ga matasa ta yadda za ka samu kaso mai yawa daga cikinsu da ba za su iya wuni ba tare da sun leƙa ba. Da yawa sanadiyyar soyayyarsu da yanar gizo kan jefa su ga mugun aiki, ko dai don sun mallaki wayoyin da ke iya ba su damar shiga lungu da saƙo na manhajojin da suke ƙawata intanet, ko kuma don siyan datar da za su yi amfani da ita.

A cikin irin wannan yanayi ne aka samu wasu haziƙan matasa da ke da hangen nesa, suka nutse a kogin basirar da Allah Ya yi masu, har suka samo hanyar da suke amfani da waɗannan kafafen da aka ƙirƙira don nishaɗi da kuma sada zumunta wurin da za su samu na rufawa kai asiri, wanda ta hakan za su samu har ‘yan kuɗaɗen da zai kula da shege da ficen su a kafafen.

Maryam Ango na ɗaya daga cikin matasan mata da suka mayar da kafar sada zumunta wurin neman na kai. A tattaunawar ta da Manhaja, za ku ji yadda ta fara da kuma irin ƙalubale da nasarororin da ta samu. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Maryam Ango:

MANHAJA: Mu fara da jin tarihinki.

MARYAM ANGO: A taƙaice dai sunana Maryam Ango, an haife ni a garin Minna, Jihar Neja. A nan na taso, na yi makarantan Hill Top Model School Minna, tun daga nursery har secondary, daga nan sai na tafi na yi diploma a fannin aikin jarida, wato Mass communication. A yanzu haka dai Ina yin digirin farko a Jami’an Ibrahim Badamasi Babangida University, Lapai Niger State.

Kenan karatu ki ka sa gaba ko ana taɓa sana’a?

Ina haɗawa da sana’ar sayar da takalma gaskiya.

Me ya sa ki ka zavi haɗa taura biyu a lokaci ɗaya, wato karatu da kuma sana’a?

Kin san yanzu rayuwar sai a hankali. Kuma mun zo zamanin da kowa yana da ɗan matsalar da yake fuskanta a rayuwa. So, ba za ka zauna ka kwashi lalurorinka ka ɗora ma wani ba. Dalilin kenan da ya sa na ga cewa, me zai hana in fara wani abinda ni ma zan taimaki kaina. Saboda dole akwai lokacin da za ka so ka yi ma kanka wani abu ba tare da ka takura ma wani ya yi maka ba. Toh, kin ga da ‘yar sana’an nan da nake yi akwai abubuwa da yawa da nake yi ma kaina ba tare da na roƙa ayi mani ba.

Shi kuma karatu kin ga shima zamani ne wanda sai ka yi karatun za a yi da kai. Shi ya sa naga akwai buqatar in haɗa guda biyun a lokacin ɗaya, kuma alhamdu lillah wanka na biyan kuɗin sabulu.

Ba mu bayanin yanayin yadda ki ke kasuwancin naki na takalma?

Na fara ne a 2020 lokacin da aka yi ‘lockdown’, kuma da Facebook na fara. Zan iya cewa ma kaso casa’in da biyar bisa ɗari na ‘customers’ ɗina daga Facebook ne. A lokacin da takalman Nijeriya ‘handmade’ na fara. Mutum zai yi oda, sai a yi mishi ‘delivery’ a cikin kwana uku. Daga nan kuma sai na fara harkan ‘foreign’ takalma. Daga bisani kuma na ƙara da ‘sneakers’. halin da ake ciki dai yanzu gaskiya babu kalan takalman da bana harkan su.

Kin yi magana kan kasuwanci a kafar sadarwa. Ko za mu iya sanin yadda kafafen sada zumunta ke taimakon musamman mata a harkar kasuwancinsu?

Gaskiya kafar sadarwa na taimakon mata a harkan kasuwanci sosai. Kamar yadda na faɗa miki a baya cewa, kaso 95 cikin ‘customers’ ɗina daga kafar sadarwa ne. Cinikayyan duk a nan ne muke yin su. Kuma yawancin mata da za ki ga suna sana’a a kafar sadarwa su ma na tabbata hakan ne. Shi ya sa yake da kyau mutum ya yi amfani da midiya da kyau. Kuma kinga da ‘social media’, ba za ki tsaya ga da ga, ‘physically’ kina magana da namiji ba. Domin akasarin cinikayyar ta rubutu ce, ya nuna abinda yake so, a aika mishi. Shikenan, kasuwanci a mutunce.

Waɗanne ƙalubale ne masu kasuwanci a kafafen sada zumunta ke fuskanta?

Dama kin san duk abinda yake da nasara dama dole a tsinci ƙalubale a ciki. Toh gaskiya yawancin ƙalubalen da muke fuskanta bai fi matsalar direbobi ba, in mutum zai aika saƙon da ba gari ɗaya ba, waɗannan akwai su sosai, ki ga ke da kayanki, kin aika saƙo amma direba na miki wulaƙanci. Wani ma in ya ga dama ki yi ta kira ya ƙi ɗauka. Wani kuma za ki zauna jiran isowar shi, sai ya isa ko mintuna masu yawa ba za a ɗauka ba sai ki ji yana ce miki shi zai koma ba zai tsaya jira ba.

Da kuma ‘customers’ da za ki ga wai mutum zai ce bai yarda da kai ba, ba wai na ce hakan ba daidai ba ne, abu ne da dole za ka duba masa, mutum ya ce, bai yarda da kai ba, ba zai aika maka kuɗin shi ba, amma sai kiga mutun ya ce, bai yarda da kai ba amma kai yana so ka yarda da shi ka aika mishi da kaya ba tare da ya biya ba. In baka yarda da ni ba, to ai kuma ban ga dalilin da zai sa ka yi min ‘message’ cewa kana son kaya ba.

Za ki ga wasu kuma sai kin gama aika hotunan abubuwan da ka ke siyarwa sai ya dawo ya ce, “I’ll get back to you.” To ka san ba ka shirya ba me ya sa zaka zo ka yi cinikin abu kamar wanda ya shirya?

Ta ya ki ke ganin za a iya shawo kan matsalolin?

Eh to, direbobi dai kam ‘yan Union ne ya kamata su sa mana baki, su dinga mana sauƙi, sannan su daina wulaƙanta mu. Duk da cewa su ma ‘yan Union ɗin ba su taimaka mana su ma, don kusan duk kanwar ja ce.

Amma dai duk da haka direbobi su ji tsoron Allah kuma su sani kasuwancin nan ‘yar taimakekeniya ce, ba wai kyauta suke kai mana kayan nan ba. Su gyara halayyansu. Mu kuma ‘entrepreneurs’ mu yi ta haƙuri da ‘customers’.

Sanar da mu irin nasarororin da ki ka samu ta hanyar sana’a.

Gaskiya na samu nasarori da yawa a wannan ‘yar sana’ar da nake yi. Yadda dai na faɗa miki a baya, duk wasu ‘yan ƙananan buƙatu na Ina yin su ba tare da na takura ma kowa ba, wannan ma kawai babban nasara ce a wurina.

Menene muhimmancin sana’a ga ‘ya mace a wannan zamani da muke ciki?

Sana’a kam na da muhimmanci sosai ga ‘ya mace, domin zata rufa ma kanta asiri, ta taimaka ma ‘yan’uwanta da iyalinta. Yana da kyau mace ta zamana ta dogara da kanta.

Mu koma ɓangaren iyali, kina da aure?

(Dariya) A’a, ba ni da aure.

A matsayinki ta matashiya, wacce shawara za ki ba matasan mata ‘yan’uwanki kan muhimmancin neman ilimi?

Yana da matuqar muhimmanci mu tashi mu nemi ilimi, domin yanzu duniyar sai kana da ilimi za ka ji daɗin ta.

A matsayinki ta mace matashiya sai kina da ilimi ne za ki iya yi ma kanki ‘decision’ ɗin da zai amfanar da ke, kama daga zaɓen abokin rayuwa, yadda za ki gudanar da rayuwarki, kare mutuncinki da dai sauransu.

Duk da makarantar akwai wahala, amma Indai kina da damar yin karatu to gaskiya ki yi karatun nan ki samu ilimi, ki kuma yi qoqarin ganin kin saka shi a alamuran rayuwarki, sai ki ga abubuwa sun zo miki da sauƙi. Kuma duk mace mai ilimi da take amfani da shi kuma ta san abinda take yi da wuya kaga an wulaƙanta ta ko kuma ana mata abinda bai kamata ba.

Ko akwai tazara tsakanin mace mai ilimi da marar ilimi?

Gaskiya kam akwai, kamar yadda na faɗi a sama, za ki ga ma yadda suke rayuwa akwai bambanci sosai.

Kuma ita mace mai ilimi ba za a wulaƙanta ta ba. Kuma daraja gare ta. Sannan a zamantakewa ma ta aure da kuma zama da mutane za ki ga duk abin ya bambanta. Dan ita mace mai ilimi duk abinda zata yi, zata yi shi ne dan ta san ya kamata.

Wane buri ki ke da shi kan sana’ar da ki ke yi a yanzu?

Gaskiya ba ni da burin da ya wuce ace yau ga shi Allah ya ba ni Iko na buɗe babban shago, yadda in mutum yana son abu, kawai zai zo inda shagona yake, ya duba abinda yake so ya ɗauka. Kin ga ma shikenan mutun ya huta da masu rashin yarda (dariya).

Wacce shawara za ki ba wa mata matasa waɗanda ke zaune ba sana’a?

Shawara ta a gare su ita ce, su kama sana’a ko da ba su da jari indai suna da waya da data, to su yi amfani da wannan damar ta zamani su nemi na kansu, kar su zauna haka nan.

Ya matsayin kwalliya ta ke ga ‘ya mace?

To, kwalliya abu ne mai muhimmanci ga ‘ya mace. Ba lallai kwalliyan fuska ba, a gan ki kin yi shigar kamala, ba tare da bayyana tsiraici ba, wannan ma kwalliya ce ta mutunci.

Wane irin kaya ki ka fi son yin kwalliya da su?

Ina son atamfa sosai. Duk wayancin kayana ma su ne, riga da skirt ko doguwar riga. Hijabai ma suna da daɗin sakawa kuma su ma in ka samu aka yi maka ɗinki mai kyau, yana fitowa da mutum sosai, kuma ba irin hijaban nan da ake ɗinkawa na zamani ba fa (dariya).

Sanar da mu irin abincin da ki ka fi sha’awa da dalili da ya sa ki ka fi son shi.

Da yake abinci bai wani dame ni sosai ba, don gaskiya zan iya ɗaukar bacci in bar abinci, amma dai Ina son plantain sosai a haɗa shi da shinkafa, duk da haka ba ni da takamaiman abincin da zan ce ga shi shi na fi so gaskiya.

Muna godiya.

Ni ma na gode sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *