Kafofin watsa labaran ƙasa da ƙasa: Taruka biyu na Sin na da babbar ma’ana ga zamantakewar al’ummun duniya

Da CRI HAUSA

Kamfanin watsa labarai na ƙasar Kenya wato KBC, ya gabatar da wani sharhi dake cewa, taruka biyu na ƙasar Sin waɗanda ke gudana a birnin Beijing na ƙasar suna jawo hankalin al’ummun ƙasashen duniya matuƙa, musamman ma batun dake shafar shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya, saboda shawarar tana amfanar dukka duniya, har ma tana taka muhimmiyar rawa wajen cuɗanyar tattalin arzikin duniya. Sharhin ya ƙara cewa, ƙasar Sin abokiyar cinikayya mafi girma ta ƙasashen Afirka ce, wadda ke zuba jari mafi yawa a nahiyar, musamman ma a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, ƙasashen Afirka suna cin gajiya daga jarin da ƙasar Sin ke zubawa a nahiyar, misali a ɓangarorin manyan ayyukan gina kayayyakin more rayuwar jama’a da kuma kiwon lafiya.

Don haka batutuwan da za a tattauna yayin taruka biyu na ƙasar Sin suna da babbar ma’ana ga ƙasashen Afirka, ban da haka, shugabannin ƙasashen Afirka da dama suna sa ran za su kara kyautata hulɗar dake tsakanin ƙasashensu da ƙasar Sin, tare kuma da ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar dake tsakanin sassan biyu.

Jaridar “Observer” ta ƙasar Pakistan ta wallafa wani sharhi a ranar 4 ga wata, inda aka bayyana cewa, ƙasar Sin ta samu amincewa daga masu zuba jari a faɗin duniya, bisa salon karuwar tattalin arzikinta na ci gaba mai dorewa, yanzu haka ana gudanar da taruka biyu a ƙasar Sin, inda ake tabbatar da cewa, idan ƙasar Sin ta ci gaba da samun wadata, tabbas ne ɗaukacin ƙasashen duniya za su ci gajiya daga ci gaban ƙasar ta Sin.

Fassarawa: Jamila