Kafofin watsa labaran Amurka: Masu zuba jari na ƙasa da ƙasa suna ƙara zuba jari ga kasuwar hada-hadar kuɗin Sin

Daga CRI HAUSA

Tashar yanar gizo dake ba da labaran sayayya da kasuwanci ta Amurka ta wallafa wani rahoto a ranar 17 ga wata dake cewa, duk da cewa, masu zuba jari dake cikin gidan ƙasar Sin ba su nuna kuzari sosai ga kasuwar hada-hadar kuɗin ƙasar ba, masu zuba jari na ƙasa da ƙasa na ƙara zuba jarinsu ga kasuwar hada-hadar kuɗin ƙasar Sin. Alƙaluma sun nuna cewa, a watan Janairun bana, adadin kuɗin da aka zuba kan kasuwar hada-hadar kuɗin ƙasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 16.6, wannan kuma shi ne karo na huɗu da adadin ya zarta dala biliyan 10 a cikin wata guda, tun bayan ɓarkewar annobar cutar COVID-19.

An lura cewa, a cikin ‘yan watannin da suka gabata, kamfanonin zuba jari dake faɗin duniya suna ƙara nuna kuzari kan kasuwar hada-hadar kuɗin ƙasar Sin, inda ƙasar ta kasance zabi mai inganci a ɓangaren zuba jari a bana.

Fassarawa: Jamila daga CRI Hausa