Kakakin majalisa da wasu jiga-jigan APC sun sauya sheƙa zuwa PDP a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA, a Sakkwato

Kakakin majalisar dokokin Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Achida, da uku daga cikin waɗanda suka so tsayawa jam’iyyar APC takarar gwamna sun sauya sheka daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP.

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP kana gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa, ne ya karɓi waɗanda suka sauya sheƙarar a babban filin wasanni na sukuwa dake Sakkwato.

Waɗanda suka sauya sheƙarar dai sun haɗa da, Abdullahi Balarabe Salame, wanda ya kasance tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Sakkwato kuma tsohon muƙaddashin gwamnan jihar da a yanzu yake zama ɗan majalisar wakilai ne mai wakiltar ƙananan hukumomin Gwadabawa da Illela, da kakakin majalisar dokokin jihar Sakkwato Aminu Mohammed Achida da Yusuf Suleiman tsohon ministan sufuri, matasa da wasanni ne kuma yake zama shugaban hukumar gudanarwa ta NAFDAC.

Sauran sun haɗa da Yusuf Isah Kurdu, memba a Majalisar Wakilai mai wakiltar Gudu/Tangaza da Sanata Bello Jibrin Gada OFR tsohon Sanatan Tarayyar Nijeriya ne kuma tsohon Minista, da kuma Aminu Bello ACY tsohon Kwamishinan Kasuwanci, yayin da shi ma Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato mai wakiltar mazaɓar Wamakko, Hon. Murtala Maigona ya bi sahun masu sauya sheƙar.

Bayan haka, akwai Hon. Abdullahi Hassan dake zamowa tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Sakkwato ta Arewa ne da Alh. A.A Gumbi Shahararren ɗan kasuwa kuma ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC da ya gabata a kwanan nan dama Hassan Sahabi Sanyinnawal babban mai magana da yawun Sanata Wamakko ne jagoran jam’iyyar APC a jihar Sokoto.

Da yake karɓar waɗanda suka sauya sheƙar, Gwamnan na Delta Okowa, ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, na da nagarta da ilimin iya tunkarar matsalolin dake addabar ƙasar nan.

“Jamiyyar mu za ta yi aiki tukuru wajen tunkarar matsalolin da ke addabar Najeriya musamman ma na tsaro da makamantansu, don haka Atiku Abubakar zai iya shawo kan matsalolin inji shi.”

Sa’ilin da yake tofa albarkacin bakinsa, Gwamna Aminu Tambuwal ya bayyana jin daɗin sa na karɓar waɗanda suka sauya shekar zuwa jam’iyyar PDP.

“A yau kun dawo gida, ina mai farin ciki kasancewa kun yi na’am da jagorancin jam’iyyar PDP a matakin jiha da ma ƙasa baki ɗaya wannan abin a yaba ne inji shi”.

Wurin taron

Don haka Tambuwal ya bayyana Atiku da Okowa a matsayin masu kishin ƙasa dake da burin ciyar da ita a gaba, yana mai cewar haɗin zai samar da kyakkyawan shugabanci da ƙasar nan ke buƙata.

Da yake jawabi tun da farko, shugaban jam’iyyar na ƙasa Iyorchia Ayu, ya bayyana cewa jam’iyyar ta soma da kafar dama gabanin nasarar lashe zaɓen shekarar 2023 da zatayi.

Ayu, wanda Amb. Umar Damagum, ya wakilta ya yi amannar cewa jam’iyyar zatayi nasara a zaɓukkan dake tafe musamman a Sskkwato da ma matakin ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *