Kalubalen da na fuskanta a aikin jarida – Madina Dauda Nadabo

Daga AYSHA ASAS

HAJIYA MADINA DAUDA NADABO gogaggiyar ‘yar jarida ce wacce ta dade tana bayar da gagarumar gudummawa wajen dauko rahotanni da watsawa a sassan duniya, kuma qwararriyar ‘yar jarida wadda take nuna qwarewar aiki wajen gabatar da shirye-shirye masu ilimantarwa, nishadantarwa gami da zaburarwa. Manhajata yi hira da ita don jin gwagwarmayar ta a fannin aikin jarida kamar haka:

Hajiya duk da ke ba boyayya ba ce wajen mutane, amma za mu so jin taqaitaccen tarihinki a taqaice.

To, Assalamu alaikum. Da farko dai suna na Madina Dauda Nadabo. An haife ni a Unguwar Shanu da ke cikin garin Kaduna Na fara karatun furamare a makarantar sojoji da ke Kaduna (NDA), na yi shekara biyu a wurin, daga bisani aka mayar da ni LEA Unguwar Sarki na kammala furamare a wurin. Bayan mun rubuta jarabawar share-fagen shiga sakandare ni da su Hauwa Dikko (Allah ya jiqan ta), da Rakiya Abba Abdulqadir. Tiri-tiri (ita ma Allah ya jiqan ta da rahama) da kuma Jummai Shedrak, duk muka ci jarabawa, kowannen mu ya ci gaba da karatu.

 Na yi makarantar sakandare da ke Titin Independence a garin Kaduna, sannan muka koma garin Maiduguri ni da iyayena na ci gaba da makarantar ’yan mata a can, wato GGSS Maiduguri. Bayan kammala karatun sakandare sai na fara aiki da gidan Rediyon Tarayya a shekarar 1980, ina karatu na ina hadawa da aiki.

Na yi Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Kaduna, na yi karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano, sannan na koma Abuja na ci gaba da karatu a cibiyar horas da ’yan jaridu da ake kira IIJ. A nan ne na samu PGD dina a kan harkar jarida, kuma na hada da wasu karance-karance a qasashen waje. Na je Jami’ar Pennsylvania inda na karanci shugabanci. Na je Afirka ta Kudu shekara uku da suka gabata a can ma na karanci shugabanci. Wannan a taqaice kenan bayan wasu kwasa-kwasai da na yi a cikin gida Nijeriya a cibiyar horas da ’yan jaridu ta gidan Rediyon Nijeriya da ke Jihar Legas, na yi kwasa-kwasai mabambanta. To su ne irin qwarewar da na samu zuwa yau.

Kin shahara a bangaren aikin jarida musamman ma a gidan rediyon Muryar Amurka. Shin tun yaushe ne ki ka fara wannan aiki, kuma zuwa yanzu wane mataki ki ke kai?

To yanzu dai na yi shekara 22 ina yi wa Muryar Amurka aiki. A lokacin da suke daukar ma’aikata sai sun turo wani wakili nasu daga Amurka ya zo nan Nijeriya ya saurari gidajen yada labarai ko kuma ya zabi wadanda yake jin shirye-shiryen su, sai a tuntubi wadannan ma’aikatun a ce masu ga abin da ake so. To a nawa sai da aka yi sau uku, shi ne Shehu Yusuf Kura mai aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka ya zo gida Nijeriya, aka ba shi wannan aiki daga can, ya dinga sauraron gidajen rediyo ya ji muryoyin da ya ke ganin za a iya daukar su aiki. Ba alfahari ba, a gidan Rediyon Tarayyar Nijeriya ni ce mace daya da aka dora wa nauyin gabatar da shirye-shiryen siyasa, da kuma gabatar da labarai a kan fannin da na qware, kuma ina yin sharhi na gidan Rediyon Nijeriya; to gaba daya Yusuf Kura sai da ya dauki wadannan shirye-shiryen nawa ya tafi da su, da ya kai musu sun ji dadin abin da suka ji qwarai da gaske, saboda haka sai suka nemi su dauke ni aiki amma a sashen Turanci a lokacin. To sai na yarda aka dauke ni aikin, ina kawo masu rahotanni a wani shiri nasu da suke yi ‘Africa Perspectives’, kuma suna yin shi ne a matsayin gudunmawa da suke ba Nijeriya na ta yi qoqarin komawa tafarkin dimokaradiyya a 1999. To mu mun fara wannan shirin a shekarar 1998 kafin mulkin dimokaradiyya. Saboda haka duk wasu shirye-shirye da hukumomin Nijeriya da mahukunta ke yi na ganin cewa an koma tafarkin dimokiradiyya din su ne ire-iren abubuwan da suka daukar mana hankali muke yin rahotanni a kan su. Kuma garin Kaduna shi ne cibiyar da duk abin da ki ke tsammani zai iya faruwa a qasar nan, cibiya ce ta siyasa, cibiya ce ta masu ilimi kuma wadanda suka san ya kamata. Firimiyan farko da aka yi a Nijeriya a Kaduna ya zauna, saboda haka Kaduna jiha ce da kowane mutum zai iya alfahari da ita idan da an bari ta ci gaba da bunqasa da daukakar da Allah ya yi mata. Don haka daga Kadunan na ke bayar da rahotanni, kuma ba a iyakance min dole sai Kaduna kadai ba, duk inda na ga labari wanda zai taimaka wa qasa ta Nijeriya wajen dawowa kan tafarkin dimokiradiyya ana yarda in dauki wannan rahoton. A cikin wata guda kawai nakan yi rahotanni ashirin zuwa ashirin da biyu, ban da kuma aikin da na ke yi a gidan Rediyon Nijeriya.

Bayan shekaru kamar biyu an yi zabe a 1999 Obasanjo ya lashe, har aka rantsar da shi ba a dakatar da wannan shirin ba har zuwa 2000 an ci gaba da yi, to daga baya sai muka canja alqiblar tunanin mu zuwa ga yadda mahukunta za su gudanar da ayyukan su da yadda za su tafiyar da ’yan qasa domin a samu daidaito a gudu tare a tsira tare.

Da aka ga dimokiradiyya ta zauna daidai sai aka dakatar da wannan shirin na ‘Africa Perspectives’, sai hukumar VOA ta ce mana dama ba ma’aikatar VOA din ce ta zuba kudi a kan wannan shirin ba don a dinga gudanar shi, wasu ’yan qasar Amurka ne wadanda ke son ganin Nijeriya ta habaka su ne suka cire kudaden su suka zuba a wannan asusun, da shi ake biyan dukkanin mu wadanda aka dauka aiki a wannan fannin. Bayan sun tabbatar da cewa burin su ya cika kuma Nijeriya ta koma tafarkin dimokiradiyya kuma ana zaune lafiya ba wata matsala, sai suka ce za su karkatar da kudin su ta wani bangaren daban. Idan ki ka duba za ki ga har yanzu attajiran Amurka irinsu Bill Gates, Markzukerberge da sauransu suna taimaka wa wasu qasashe a Afirka, ciki kuwa har da nan Nijeriya.

Saboda haka ban dai fasa aiki da VOA din ba, sai suka fahimci cewa akwai wata basira da qwarewa da na ke da ita, ga shi ina dan jin Hausa duk da dai ba karanta ta na yi ba, amma suna ganin zan dace da wakiliyar Sashen Hausa tunda an daina yin wancan shirin, ba a son a rasa mu gaba daya. Shi ne sai suka dauke ni daga sashen turanci zuwa Sashen Hausa a shekarar 2000. Shekara 22 ke nan ina aiki da VOA, sashen Hausa kuma shekara ta 20 da su kenan. Har yanzu kuma ina yi, ni ce mai dauko labarai a Majalisar Dokokin Nijeriya kuma tun lokacin da na fara a wajen na ke. Saboda yawan kawo rahotanni da mu’amala da ’yan siyasa da cudanya da su ya sa ko da sun shiga zantawar sirri ne a siyasance, ko jam’iyyance ko ta hadin gwiwa na kan fahimci abubuwan da za su tattauna a kai kuma hasashena ya kan zama gaskiya har in watsa shi a rahotanni na, duk saboda mu’amala da su, saboda ina tare da su kullum, ina zaune tare da su a zauren majalisa, na san abubuwan da ake tattaunawa kullum, na san masu kishin cikin su da dai sauran su.

In taqaita miki dai yanzu ni ce jagorar wannan cibiya ta Muryar Amurka da ke babban birnin tarayyar Nijeriya.

A matsayin ki na mace ’yar jarida, shin wane irin qalubale ki  ke samu a cikin aikin?

To gaskiya akwai qalubale. Kin ga dai da farko lokacin da na fara aiki a gidan Rediyon Tarayya, an dauke mu kusan mu shida masu gabatar da shirye-shirye da karanta labarai a fannin Turanci, to  ba zan ce ni ce na fi kowa ba, amma na yi fice sosai, domin marigayi Dan’iyan Zazzau, Alhaji Yusuf Ladan, shi ne wanda na fara aiki a qarqashin sa yana matsayin manaja a sashen shirye-shirye a gidan rediyon. Wata rana ya shigo ya same ni ina ayyuka na, ya ce min sun ji dadi da suka dauke ni aiki ga ni yarinya amma kuma ina da natsuwa domin ina yin aikin daidai yadda ya kamata. Da aka tashi tura mu horaswa a cibiyar horas da ’yan jaridu na gidan Rediyon Tarayya da ke Legas, na yi kwasa-kwasai da dama a wajen. Da na dawo sai na shugabanci fannin gabatarwa na gidan rediyon tarayya. Saboda haka sai ya zamto wasu na jin dadi wasu kuma a’a suna ganin a matsayi na na mace kuma ’yar Musulmi bai kamata in dinga zuwa gidan rediyo ana jin murya ta ba, murya ta al’aura ce, kada a ji ni, gwamma in yi aiki a wani fannin daban ya fi, amma wai ina yi kullum ana ji na. Saboda haka sai na tambayi malamai don jin menene aibun wannan aiki ga ’ya mace; to malaman da na tambaya kowanne fatawar sa daban, wasu sun ba ni qarfin gwiwa sosai.

Sai kuma qalubalen wasu mazan da suke ganin ai ke ’ya mace ce ba za ki iya ba, kina da rauni. Sai muka ga cewa a wajen horaswa din ma kawai mun fi wasu mazan qwazo da himma, saboda haka ni yanzu haka ina alfahari da wannan aikin tunda na fara tun ina ’yar yarinya.

Wadanne nasarori kika samu a wannan aiki na jarida?

Kamar yadda na fada miki a baya cewar na fara aikin jarida lokacin da na kammala sakandare har zuwa yanzu, kuma kin ga ni ce shugabar Muryar Amurka a nan birnin tarayya Abuja, to wannan ma babbar nasara ce, tunda na fara aiki ne tun kafin in ci gaba da kwaleji ko jami’a. Duk da qalubalen da na ke samu kuma ban tsaya da aiki ba, ban kuma tsaya da karatun ba.

Ko akwai wani tsari da kika sani a aikin jarida wanda kuke amfani da shi a can baya wanda yanzu aka daina amfani da shi ko aka watsar?

Akwai tsare-tsare, kamar tsarin aiki, kin ga yanzu wata ’yar na’ura ce qarama da muke amfani da ita wajen daukar murya amma a da ba haka ba ne. Sa’annan yanzu ana amfani da yanar gizo, kamar hirar nan da muke yi da ke a yanzu za ki iya tura ta qasar Amurka cikin daqiqa hudu zuwa biyar, ba kamar da ba.

A sha’anin aikin ki, wane abu ne ya fi ba ki mamaki ko ya fi tsoratar da ke?

To, gaskiya ni babu abin da ya ba ni mamaki ko ya tsoratar da ni, saboda ko da na gama sakandare ban fara aikin ba sai da na samu horaswa ta watanni uku.

Wace shawara za ki ba mata masu sha’awar aikin jarida da kuma wadanda suke a kai yanzu?

To, mata masu koyon aikin jarida ina roqon ku duk abin da za ku yi ku yi tunanin abubuwa biyu zuwa uku; addinin ku, makomar ku da kuma tunanin inda ku ka fito, wato gidajen ku. Ku yi duk aikin da za ku yi cikin kamun kai, sannan ku tabbatar cewa kun yi karatu mai yawa. Mace ta sunkuyar da kanta ta koya, amma ba ki qasqantar da kan ki ba. Ki kiyaye addinin ki, duk abin da za ki yi ki dinga tunanin Allah na kallon ki.

Wane rahoto kika fi sha’awa da jin dadin kawowa a aikinki na jarida?

Kamar yadda na fada miki, ina son in ga ’ya mace ta yi karatu kuma ta riqe mutuncin kan ta, saboda haka na fi son kawo rahoton da suka shafi zamantakewa da mu’amalar ‘ya’ya mata.

Vangaren iyali fa akwai su?

E, ina da miji na, sunan shi Alhaji Zakari Ya’u Yusuf Nadabo, wanda shi ne mataimakin darakta a Rediyon Tarayyar Nijeriya.

Wane abinci ki ka fi so?

Kai, ina son abinci da yawa! Kamar tuwon shinkafa da miyar taushe, ina son sinasir ko masa da miyar taushe, kuma ina son cin sakwara da miyar ogbono.