Kamata ya yi ƙasashen dake da tarin makaman nukiliya su fara ragewa bisa adalci inji wani jami’in Ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA

Jami’in hukumar dake lura da warware makaman nukiliya ta ƙasar Sin Fu Cong, ya ce kamata ya yi ƙasashen dake da tarin makaman nukiliya su wuce gaba, wajen rage makaman yaƙi da suke da su, a fayyace, tare da kaucewa sake ƙara mallakar wasu, kuma su yi hakan bisa tsarin doka.

Jami’in ya bayyana hakan ne ga mahalarta taron bita, na sassan da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya karo na 10. Yana mai cewa “Yayin da ake kwance ɗamarar makaman nukiliya, kamata ya yi a wanzar da daidaito tsakanin ƙasa da ƙasa, da samar da tsaro mai dorewa ga kowa”.

Fassarawar Saminu Alhassan