Kamfanin Ɗangote ya ba wa manoma 60 tallafin noma

Daga AMINA YUSUF ALI

A ƙoƙarinsa na bunƙasa harkar noma wadataccen abinci a yayin damina a ƙasar nan, kamfanin Ɗangote ya sanar da ba da tallafin noma ga manoma 60 da suke a yankin Ibese.

A wani jawabi da kamfanin ya saki ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata, kamfanin ya bayyana cewa, tallafin zai taimaka wajen ƙara musu ƙarfin iya yin noma na zamani don samun ƙarin wadatattun amfanin gona masu inganci.
Hakazalika, hukumar gudanarwar kamfanin sun bayyana cewa, wannan shirin musamman an yi shi saboda manoman masara.

Azad Nawabuddin, Daraktan reshen kamfanin na reshen Ibese, an zaɓo manoman ne daga dukkan garuruwan da kamfanonin sumuntin suke da rassa guda 17. Wannan ita ce yarjejeniyar da aka ƙulla a tsakanin kamfanin al’ummar yankunan wadda ɓangarorin suka sanya wa hannu a kwanan nan.

Mista Nawabuddin ya qara da cewa, kamfanin kuma a shirya yake a kullum ta kowacce fuska don bunƙasar samar da isasshen abinci.

Hakazalika ya bayyana wa manoman cewa, kamfanin sumuntin zai haɗa gwiwa da ƙwararru don tsara bita ta horaswa ga manoma a kan sanin makamar aiki game da albarkar ƙasa don inganta noman masara.

Haka a cewar sa, kamfanin ba zai tsaya a matakin horaswa kaɗai ba, zai taimaka wa manoma da gyare gona, rarraba iri, maganin ƙwari, da taki da sauransu. Har ma da nuna musu hanyoyin samun ciniki.