Kamfanin Blueprint ya ɗage babban taronsa na shekara-shekara

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Gudanarwar ta Kamfanin Jaridun Blueprint, ta ba da sanarwar ɗage taron laccar da kamfanin ya saba shiryawa da kuma miƙa lambobin yabo shekara-shekara wanda da fari ta tsara gudanarwa ranar Alhamis, 23 ga Yuni, 2022.

Sanarwar ɗagewar na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labaran da Babban Jami’in Gudanarwar kamfanin, Malam Salisu Umar, ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Jami’in ya ce, za a sanar da sabon lokacin da taron zai gudana nan ba da daɗewa ba.

Ya ƙara da cewa, an ɗage taron ne saboda taron ECOWAS/NEC da zai gudana a ranar Alhamis wanda hakan ya sa gwamnonin da ya kamata su halarci taron lacca ɗin ba za su samu zuwa ba.

A madadin kamfanin, Malam Umar ya ba da haƙuri kan duk wani akasin da ɗage taron zai haifar wa jama’a.