Kamfanin Boska ya gudanar da aikin jinya kyauta a Jihar Sakkwato

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

A ƙoƙarin da kamfanin Dexa Medical masu yin Boska ke yi na duba lafiyar mutane a ranar Asabar ɗin da ta gabata, 20 ga watan nan na Agusta, kamfanin ya gudanar da aikin jinya kyauta ga al’ummar Kwannawa dake ƙaramar hukumar Denge Shuni a Jihar Sakkwato.

A jawabinsa ga jama’ar da suka ci gajiyar shirin kamfanin na Dexa, shugaban shiyya na kamfanin na yankin Sakkwato Adeyemi Afeez Ola, cewa ya yi kamfanin ya ware wannan ranar ce don taimakawa jama’a masu larurar gani da masu fama da wasu ƙananan cututtuka da za a yi wa aikin ido a ba su gilashi da magunguna kyauta.

Adeyemi Afeez Ola, ya ce kafin wannan rana sun ji ra’ayoyin mutane kan irin matsalar su shi ya sa a wannan karo suka shirya taron a garin Denge Shuni, a jihar Sakkwato, don a duba lafiyar idanunsu a ba su magunguna da gilashi kyauta.

Ya ce kimanin mutane ɗari bakwai ne suka ci gajiyar shirin inda ya ce shirin zai ci gaba a sauran jihohin ƙasar nan, inda a ranar Juma’a mai zuwa zai gudanar da irin wannan aiki a Jihar Bauchi, Arewa maso Gabashin Njeriya.

Ya kuma ce dalilin ware wannan rana don duba lafiyar idanu kyauta da sauran cututttuka, shi ne suna so ne su ji daga kwastomominsu da suke amfani da maganinsu na Boska sannan su ga kuma ta yadda za su taimaka musu a jihohi 7 na faɗin tarayyar ƙasar nan a cikin wannan shekara ta 2022.

Ya kuma qara da cewa ɗaruruwan mutane ne a ciki da wajen garin Dange Shuni a yankin Kwannawa magidanta ‘yan kasuwa da sauran al’ummar gari har ma da matafiya ne suka ci gajiyar shirin nasu.

Wasu daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin da suka haɗa da Nasiru Dauda Abba, da Shehu Mohammad da Maryam Abduljalil da Sakina Yusuf, yaba wa kamfanin suka yi sannan suka yi kira da cewa su faɗaɗa shirin daga kwana ɗaya zuwa kwanaki uku domin ƙara taimakon al’umma musamman marasa galihu.

Sannan suka ƙara gode wa kamfanin bisa wannan ƙoƙari na su na duba lafiyar idanu da bada tabarau gami da magunguna kyauta a wannan rana da suka ware ta musamman ta ranar Boska Day Campaign Free for Health Care Services da cewa ya kamata gwamnati ta bai wa kamfanin lambar yabo domin matsalar ido ita ce ke damun mutane da dama kuma basu da yadda za su yi.