Daga AMINA YUSUF ALI
A ranar Talatar da ta gabata ne dai kamfanin Google ya ba da sanarwar naɗin wani ɗan Nijeriya, Alex Okosi a matsayin Manajan Darakatan Google na Afirka domin taimaka wa kasuwanci da tattalin arziki su bunƙasa.
Mataimakin Shugaban EMEA na Google, Meir Brand shi ya hayyana hakan a wani jawabi. Sannan ya ce, a yanzu Mista Okosi shi ne zai ja ragamar ayyukan Google a Afirka.
Mista Brand ya ƙara da cewa, wannan muƙami kuma zai taimaka wa biliyoyin masu amfani da shafin na Google su samu ƙarin abubuwa daga gare shi.
“Alex shugaba ne na haƙiƙa mai tarin gogewa a fannin yaɗa labarai da kuma masana’antar fasaha. Yana da kyakkyawar fahimta a kan ƙasashen Afirka da kuma shauƙin amfani da fasaha wajen tallafa wa mutane da kasuwanci,” inji Mista Brand.
Kafin wannan naɗin, ya riƙe muƙami a YouTube, sannan Mista Okosi riƙe muƙamin Mataimakin shugaban zartarwa kuma manajan daraktan kamfanin haɗakar kafofin yaɗa labarai na duniya na Viacom Afirka da kuma BET.
A muƙaminsa na baya na YouTube, Mista Okosi ya yi ƙoƙari wajen ciyar da da dandalin gaba da faɗaɗa shi a faɗin Afirka, Gabas ta Tsakiya, da Turkey.
Bayan naɗin nasa, Mista Okosi ya nuna farin cikinsa na samun wannan muqami a matsayin shugaban tawagar Google na Afirka bakiɗaya, kuma ya ce dama ce da zai samu kusanci da wannan yanki da yake tsananin ƙauna wato Afirka.
Mista Okosi ya ce, ya yi imanin cewa harkar fasaha da musamman intanet suna da muhimmanci kuma za su taimaka wa rayuwar mutane da kasuwanci don su bunƙasa a Afrika.
A cewarsa, Google tana yin ayyukanta a Afirka fiye da shekaru 10 kuma tana da rassa a Ghana, Kenya, Nijeriya da kuma Afirka ta kudu. Kuma mutane miliyoyi ne suke amfani da kayansu da da kuma ayyukansu kullum a Afirka.