Kamfanin ‘Google’ zai zuba Dala biliyan guda don bunƙasa fasahar zamani a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

Kamfanin Google ya bayyana cewa, zai ƙara zuba jarin Dalar Amurka har biliyan guda domin ganin an bunkasa fasahar zamani ta yanar gizo a Nijeriya da wasu ƙasashen Afirka.

Kamfanin ya bayyana cewa, wannan yunƙurin nasa na zuba jari zai sa a samu rangwamen farashin yanar gizo da kaso 21. Sannan zai ninka ƙarfin yanar gizo sau biyar a ƙasar Nijeriya.
 
Wannan bayani ya fito daga bakin Manajan Daraktan Google na Afirka, Nitin Gajria. A lokacin taron Google na Afirka na farko wanda aka gudanar a Larabar nan da ta wuce. A cewar sa, Kamfanin Google a shirye yake domin kawo cigaban mutane  da harkar kasuwanci da ilimi a Afirka.

Gajria ya ƙara da cewa, Google sun yi matuƙar ƙoƙari domin ganin kowa ya samu hawa yanar gizo a sauƙaƙe. Inda a yanzu haka a cewarsa tuni shirye-shirye sun yi nisa na buɗe tashar Equiano wacce za ta dinga haɗa Afirka da ƙasashen Turai.

A yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa na samar da rassanta a ƙasashen, Nijeriya, Namibia, St Helena, da kuma Africa ta Kudu.