Kamfanin lantarki da bankuna sun fi kowa shan ƙorafi a 2021 – Bincike

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar kare haƙƙin masu saye  (FCCPC) ta bayyana cewa, Kamfanin wutar lantarki ya sake yin zarra a karo na biyu a matsayin kamfanin da ya fi kowanne amsar ƙorafi kamar dai yadda ya yi a shekarar bara ta 2020 ya sake yi a bana ma. 

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ya rawaito cewa, Shugaban zartarwa na  FCCPC, Mista Babatunde Irukerashi ne bayyana haka a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja. Inda ya bayyana cewa, sashen banki shi ne ya biyo bayan kamfanonin lantarkin a matsayin na biyu wajen amsar ƙorafi. 

Sannan su kuma kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama da kamfanonin sadarwa suke rufa musu baya. 

Irukera ya bayyana cewa, hukumar tasu ta FCCPC ta amshi aƙalla ƙorafe-ƙorafe dubu talatin da biyu a cikin shekarar 2021 amma a cewar sa, hukumar ta warware kaso 80 na ƙorafe-ƙorafen da suka zo gabanta. 

Inda ya bayyana cewa: “kamfanonin da suka samu ƙorafi ma fi yawa, muna da na wutar lantarki na farko, sai bankuna sun zo na biyu, sai kuma kamfanin jirgin sama da na sadarwa su ne suke rige-rigen zuwa na uku”. Inji shi.

Ya ƙara da cewa, babbar matsalar kamfaninin jirgin sama ba wai ma ɓangaren abin hawa ba ne, rashin amana ne. Da ya haɗa da ƙin dawo wa da fasinja kuɗinsa idan an samu matsala.

Kuma a cewar sa  da ma ƙorafi a kan lantarki ba wani sabon abu ba ne a Nijeriya. Domin kwastomomi sun daɗe suna ƙorafi a kan yadda suke biyan maqudan kuɗaɗe kuma a kasa biya musu buƙatunsu yadda ya kamata. 

Daga ƙarshe, shugaban FCCPC ya bayyyana cewa, har yanzu dai hukumar tana nan tana ƙoƙarin saita al’amura da kuma samar da mafita ga ƙorafin da mutane suke kawo mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *