Kamfanin NNPC ya wanke kansa bisa ƙarancin fetur da ya game Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

A ƙarshen makon da ya gabata ne aka wayi gari da dogayen layuka a gidajen mai, a wasu jihohi a Nijeriya. Hakan ba ya rasa nasaba da irin matsanancin ƙarancin man fetur, da dangoginsa a ƙasar. Inda wasu gidajen man duk an kulle su, wasu kuma ba sa buɗewa sosai. 

Matsalar man fetur ɗin ta zo ne bayan wasu zantuka da ake yayatawa da ake kyautata zaton daga bakin dillalan man fetur ɗin suka fito. Inda aka bayyana cewa, za a samu ƙarin farashin man.

Ita a nata ɓangaren, hukumar kula da man fetur NNPC, ta wanke kanta. Inda ta bayyana sam wannan matsalar ba daga gare ta take ba. Kuma ƙarin kuɗin fetur ba ya cikin ajandar gwamnatin tarayya a yanzu.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ‘yan kwanakin nan, mutane da dama a Birnin Tarayyar Abuja sun dogara ne da ‘yan kasuwar bunburutu don samun man da za su sanya a ababen hawansu da kuma injinan janaretonsu. 

A jihar Kano kuma, ko da kuɗinka sai da rabonka. Domin kowanne gidan man dogayen layuka kawai kake gani. Kuma gidajen mai da dama a garƙame suke, ba sa aiki. Waɗanda suke buɗen ma ƙalilan ne suke iya sayar da shi a kan farashin gwamnati (167). Domin wasu wuraren ma har a kan sayar da galan a Naira 1,100 abinda ba ya wuce Naira 700 a baya.

Su kuma a nasu ɓangaren, ƙungiyar dillalan man fetur (IPMAN) ɗin, sun ɗora laifin kacokan a kan manyan kamfanonin man fetur masu zaman kansu da cewa su ne suka tsawwala farashin kamar yadda shugaban ƙungiyar ta (IPMAN),Bashir Danmallam, ya  Bayyana. 

Inda ya ƙara da cewa, a yanzu haka suna ɗauko man fetur a kan N148 zuwa N153 da N155 kowacce lita a wajen kamfanonin masu zaman kansu. Shi ya sa dole a sayar da tsada. A don haka ya ce suna kira ga gwamnati da hukumar NNPC su taka wa abin burki. 

Shi ma jami’in hulɗa da jama’a na hukumar NNPC, Garba Muhammad ya bayyana cewa kada al’umma su tashi haakalinsu farashin mai yana nan gwamnati kuma ba ta da niyyar ƙari. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *