Kamfanin sarrafa ƙarafa na Sin ya daddale yarjejeniyar haƙar ma’adinan ƙarfe a Kamaru

Daga CMG HAUSA

Reshen kamfanin sarrafa ƙarafa na ƙasar Sin dake ƙasar Kamaru da ma’aikatar kula da haƙar ma’adinai, da masana’antu, da nazarin fasahohi ta ƙasar Kamaru sun daddale yarjejeniyar haƙar ma’adinan ƙarfe a ƙasar Kamaru da jarin da aka zuba a fannin wanda ya kai fiye da dalar Amurka miliyan 700.

Ministan kula da haƙar ma’adinai, da masana’antu, da nazarin fasahohi na ƙasar Kamaru Gabriel Dodo Ndoke, da manajan reshen kamfanin Zheng Zhenghao sun daddale yarjejeniyar.

Bisa bayanin da kamfanin sarrafa ƙarafa na ƙasar Sin ya yi, yarjejeniyar ta hada da aikin haƙar ma’adinan karfe dake birnin Kribi na kudancin ƙasar Kamaru. Bayan da aka fara aikin, ana sa ran, nauyin ƙarfe da ake tacewa da kashi 60 cikin ɗari a shekara ɗaya zai kai ton miliyan 4.

Minista Dodo ya bayyana cewa, wannan aiki zai sa ƙaimi ga samun moriyar tattalin arziki da kuma bunƙasuwa mai ɗorewa. A matsayin wani kamfanin dake aiwatar da ayyukansa a ƙasa da ƙasa, kamfanin sarrafa ƙarafa na ƙasar Sin yana da fasahohi da kuɗi, ya samar da kyakkyawar dama ga ƙasar Kamaru wajen samun bunkasuwa.

A nasa ɓangare, Zheng Zhenghao ya bayyana cewa, aikin haƙar ma’adinan ƙarfe zai sa kaimi ga ƙasar Kamaru na samu kuɗin shiga, kana zai samar da ayyukan yi ga mutane kimanin 600 a ƙasar kai tsaye.

Fassarawa: Zainab