Kamfanin takin Ɗangote zai bunƙasa harkar noma a Nijeriya – Buhari

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ce da ta gabata ya ƙaddamar da kamfanin yin takin zamani na hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Ɗangote, wanda zai riƙa samar da tan-tan na takin zamani na ‘Urea’ ruɓin miliyan uku a kowace shekara, inda Shugaba Buhari ya bayyana ƙwarin gwiwar kamfanin zai yi matuƙar bunƙasa ayyukan gona a ƙasar nan.

Sabon kamfanin sarrafa takin zamanin da Shugaba Buhari ya ƙaddamar tare da shaidawar gwamnoni 18 na ƙasar nan, ministoci da jiga-jigan ‘yan kasuwa na ƙasar nan, haɗi da fitattun sarakunan gargajiya, an gina shi ne a farfajiyar Ibeju, Lekki dake harabar masana’antu na garin Ikko, kuma kusa da kamfanin tace man fetur na Ɗangote.

Shugaban ƙasa ya bayyana cewar, samar da wannan katafaren kamfani, zai samar da ɗimbin ayyukan yi wa jama’ar ƙasar nan, haɗi da kasuwanci, ma’ajiyoyi, safara da makamantan su.

“Kamfanin takin zamanin na Ɗangote, kamar yadda shugaban ƙasa ya ce, zai kuma samar da arziki wa jama’a, rage zaman kashe wando ko talauci, kana ya zama tagomashi na bunƙasar ƙasar nan.”

Kamar yadda ya yi furuci, gwamnatin tarayya a yanzu a shirye take ta samar da kyakkyawan yanayi na samar da bunƙasa zuba jarin kasuwanci a ƙasar nan, ya ƙara da cewar, gwamnatin sa za ta cigaba da samar da sinadaran bunƙasa tattalin arziki, kamar samar da kadarku, wutar lantarki, tsaro, haɗi da wanzar da dokoki da ƙa’idoji da suka dace da zuba jari wa tattalin arzikin ƙasar nan.

Shugaban Ƙasa Buhari ya kuma jaddada aniyar gwamnatin tarayya na haɗa hannu da ‘yan kasuwa ta hanyar shirin samar da harajin kamfanoni domin gyare-gyare da inganta hanyoyin safara a ɗaukacin faɗin ƙasar nan, a ƙarƙashin dokar shugaban ƙasa mai lamba 7.

“Kamar yadda dukkanin mu muka sani, samar da kyawawan hanyoyin safara sukan taimaka matuqa gaya wajen sauƙaƙa safarar kayayyaki da makamantan su a cikin ƙasa, suna kuma rage kudin gudanar da kasuwanci, haɗi da bunƙasa wadatar arziki. Muna kuma farfaɗo da hanyoyin jiragen ƙasa da gina waɗansu sabbi, domin su rage yawan aiyuka da hanyoyin safarar motoci keyi, haɗi da bunƙasa walwalar safara a ɗaukacin faɗin ƙasar nan.”

A nasa jawabin, shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Dagote ya bayyana sabon kamfanin na sarrafa takin zamani a matsayin wani canjin salon kasuwanci, domin kamfani yana da ƙarƙashin wadata Nijeriya da takin zamani, har ma da samun rarar da za a fitar zuwa ƙasashen ƙetaren a kasuwannin ƙasashen Afirka da wasu sassa na duniya.

Ya bayyana cewar, tuni ma takin Ɗangote ya shiga kasuwanni na ƙasashen Amurka, Birazil da Mexico.

Kamar yadda Ɗangote ya zayyana, kamfanin takin zamanin wanda shine mafi girma dake sarrafa takin Urea a faɗin nahiyar Afirka, an gina shi akan fili mai murabba’in kadada 500 kuma kan jimlar kuɗi Dalar Amurka biliyan biyu da rabi da ake sanya ran zai rage rashin aikin yi ko zaman kashe wa ɗimbin matasan ƙasar ta hanyar samar da ayyuka, tun daga ayyukan sarrafa takin, har zuwa safara da kasuwancin sa, dako da sauran su, haɗi da wadatar da taki ga manoma.

Shi ma da yake yin jawabi a wajen buɗe kamfanin, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana cewar, Aliko Ɗangote yana bin ƙasar nan bashi bisa wannan gagarumin aiki na ƙara tagomashi wa tattalin arzikin ƙasar nan.

Emefiele ya jinjina wa Shugaba Buhari bisa samar da goyon baya da ake buqata na tallafa wa wannan kamfani da ingantattun manufofin tattalin arziki da suka dace na kafa wannan kamfani wanda ya zo akan gaɓa, yayin da farshin alkama, takin zamani da gurɓataccen man fetur suka yi tashin gwauron zaɓi da kashi 20 cikin ɗari, biyo bayan ɓarkewar yaƙi tsakani Russia da Uknraine.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *